Imam Al-Barnawiy da Sauran Kwamandojin ISWAP Sun Arce Bayan Boko Haram Sun Kwace Sansanoninsu

Imam Al-Barnawiy da Sauran Kwamandojin ISWAP Sun Arce Bayan Boko Haram Sun Kwace Sansanoninsu

  • Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kwace manyan sansanonin takwarorinsu na ISWAP da ke Abadam a jihar Borno
  • Wannan lamarin ya sanya Ima Abou Moussab al-Barnawi da wasu manyan kwamandojin ISWAP fecewa don tseratar da rayukansu
  • Kamar yadda aka gano, ana cigaba da karon batta tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP wanda ke kawo asarar rayukan 'yan ta'addan

Borno - Kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad sun kwace wasu manyan sansanonin mayakan ta’addanci na ISWAP da ke Abadam a jihar Borno.

Wannan na zuwa ne sakamakon mummunan arangamar da sue gi a yankin Arewa maso Gabas na tafkin Chadi wanda ya tirsasa Imam na ISWAP, Abu Moussab al-Barnawi da sauran kwamandojin su tsere.

Taswirar Borno
Imam Al-Barnawiy da Sauran Kwamandojin ISWAP Sun Arce Bayan Boko Haram Sun Kwace Sansanoninsu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Cigaba da kai farmaki sansanonin yana samun jagorancin Shugaban Boko Haram, Abu Umaimah ko Bakoura Doro tare da wasu kwamandojin ‘yan ta’addan da mayakansu ya janyo mutuwar sama da ‘yan ISWAP dari a cikin mako daya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Mutum 20 Da Cikinsu Za'a Zabi Sabon Akanta Janar, FG

Mummunan farmakin ya fara ne ranar 31 ga watan Disamban 2022 bayan tsagin JAS sun kai farmaki kan ma’adanar makaman ISWAP a Toumbum Allura Kurnawa da Kangar inda suka fi karfin mayakan ISWAP bayan musayar wuta ta sa’o’i 14 wanda ya janyo mutuwar mayaka masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani makamanciyar arangama ta ranar 2 ga watan Janairu, Ali Ngulde, Amir Jaysh na JAS, ya jagoranci kwamandoji biyar da suka hada da Muke daga Mandara Mandara, Ali Ghana daga Ngauri, Abban Tukur daga Mantari da Maimusari da Abu Isa inda suka farmaki ISWAP tare da halaka da yawansu tare da tarwatsa ababen hawarsu.

A ranar 8 ga watan Janairu, mayakan Boko Haram sun farmaki wani sansanin ISWAP wanda ke arewacin Kayowa da Toumbun Gini inda suka halaka a kalla mayakan ISWAP 35 yayin da wasu mayakan da yawa suka jigata.

Kara karanta wannan

Daga karshe, an bindige wadanda ke samowa 'yan bindigan Arewa makamai

Majiyoyin sirri sun sanar da Zagazola Makama cewa mayakan Boko Haram sun fatattaki mayakan ISWAP ta wuraren Kangarwa da Dogon Chuku tare da halaka wasu.

Majiyoyin sun ce manyan kasuwannin ISWAP da ke Toumbum Gini sun JAS sun kwace su yayin da aka yi garkuwa da ‘yan mata hudu da ake zargin matan mayakan ISWAP ne a kauyen Kaula.

Majiyoyin sun ce kwace sansanin tsarin ISWAP da suka hada da wuraren makamansu da ababen hawansu ya tirsasa mayakan ISWAP din har da kwamandojinsu da suka hada da Abu Moussab Albarnawi suka tsere don gudun rasa rayukansu.

Majiyoyin sun ce Al-Barnawi ya tattara komatsansa tare da komawa Kudancin jihar Borno wuraren Gol da Chillaria a karamar hukumar Damboa inda Abba Shuwa ya karbesu.

Borno: Boko Haram sun halaka mayaka 35 na ISWAP

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto yadda mayakan ISWAP 35 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon arangamarsu da mayakan Boko Haram.

An gano cewa, rikicin da suka dade suna yi na shugabanci na cigaba da kamari inda ya kai ga kungiyoyin ke bibiyar juna tare da halaka mayakansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel