Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Magaji, Ya Kwanta Dama

Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Magaji, Ya Kwanta Dama

  • Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kwara, Honorabul Olawoyin Magaji, ya riga mu gidan gaskiya
  • Majalisar dokokin jihar ce ta tabbatar da wannan babban rashi wanda ya faru a farkon awannin ranar Litinin 9 ga watan Janairu, 2023
  • Sanarwan da aka raba wa manema labarai a Ilorin ta nuna cewa za'a masa Janaza da misalin karfe 4:00 na yamma

Kwara - Majalisar dokokin jihar Kwara ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin shugabanninta, Olawoyin Magaji, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Magaji, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kwara ya rasu ne da safiyar ranar Litinin 9 ga watan Janairu, 2023.

Zauren majalisar dokokin jihar Kwara.
Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Magaji, Ya Kwanta Dama Hoto: punchng
Asali: Depositphotos

Shugaban kwamitin tattara bayanai, matasa, wasanni da wuraren bude ido na majalisar, Awolola Olamide Ayokunle, shi ne ya tabbatar da rasuwar, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hawaye Yayin Da Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya Na PDP Ya Rasu A Abuja

A wata sanarwa za Oyunkunle ya raba wa manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar Kwara ranar Litinin, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Majalisar dokoki na takaicin sanar da rasuwar Honorabul Magaji Olawoyin, mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta tsakiya kuma shugaba a majalisar dokoki."
"Mutuwar dan majalisar ta ba zato ba tsammani ta faru ne a farkon awannin ranar Litinin 9 ga watan Janairu, 2023 bayan fama da rashin lafiya ta dan gajeren lokaci."

Majalisar ta bayyana lokacin da za'a masa Jana'iza

Sanarwan ta kara da bayanin cewa da yammacin yau Litinin za'a yi wa mamacin Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

"Za'a yi wa marigayin Jana'iza da misalin karfe 4:00 na yammacin yau Litinin a gidan iyalansa da ke Magajin Geri, yankin Surulere a Ilorin, babban birnin jihar Kwara."

"Muna fatan Allah SWT ya sa Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa," Sanarwan ta bayyana.

Kara karanta wannan

Matsalar Shugabanci Yasa An Rufe Masallacin Dr Ahmed BUK

PDP ta yi babban rashi a Bayelsa

A wani labarin kuma Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Sanatan PDP Ya Mutu a Asibitin Birnin tarayya Abuja

Inatimi Spiff, tsohon Sanata wanda ya wakilci mazabar Bayelsa ta gabas a majalisar dattawan Najeriya ya mutu bayan fama da rashin lafiya ta dan lokaci kankani.

A wata sanarwa da mai magana da yawunta ya fitar. Jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta ce mutuwar Sanata Spiff ya jefa jam'iyyar cikin bakin ciki da alhini.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel