Zaben 2023: Gwamnan APC Ya Ce Kudu Za Ta Shugabanci Najeriya Shekaru 8 Masu Zuwa

Zaben 2023: Gwamnan APC Ya Ce Kudu Za Ta Shugabanci Najeriya Shekaru 8 Masu Zuwa

  • Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya ce yanzu lokaci ne da kudancin Najeriya za ta samar da shugaban kasa
  • Akeredolu ya kuma ce shekaru takwas kudu za ta yi tana mulkin kasa saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shekara takwas
  • Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya bayyana hakan ne a Akure wurin nadin sarautar Cif Olu Falae

Ondo, Akure - Gwamna Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya ce, lokacin kudu ne, za ta fitar da shugaban kasa na shekaru 8 masu zuwa, Vanguard ta rahoto.

Akeredolu ya bayyana cewa ya zama dole a cigaba da gwagwarmayar ganin kudancin kasar ta samar da shugaban kasa har sai an cimma nasara.

Gwamna Akerodolu
2023: Mutumin Kudu Zai Shugabanci Najeriya Shekaru 8 Masu Zuwa, Akeredolu. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a Akure yayin da ya tarbi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a gidan gwamnati, Alagbaka, Akure.

Kara karanta wannan

Yadda Bola Tinubu Ya Kawo Karshen Mummunan Rikicin Jam’iyyar APC Cikin Ruwan Sanyi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amaechi ya tafi Akure ne domin mika sandan mulki ga Cif Olu Falae a matsayin Olu na Ilu Abo, a karamar hukumar Akure ta Arewa.

Akeredolu, ya bukaci mutane su zabi dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu saboda adalci da daidaito.

Ya yi bayanin cewa tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shekara takwas, yanzu lokacin kudu ne ta yi mulki na shekara takwas nan gaba.

Babu dan kishin APC da zai manta da gudunmawar Amaechi - Akeredolu

Da ya ke jinjinawa Amaechi, gwamnan ya ce babu wani dan kishin APC da zai iya manta rawar da Amaechi ya taka a matsayin direktan kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar a 2015.

Ya gode wa tsohon ministan saboda zuwa Akure don karrama Cif Falae, ya kara da cewa basaraken ya hidimtawa Najeriya sosai kuma yana alfahari da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Yankin kudu ya kamata mulkin Najeriya ya koma a 2023

A wani rahoton, Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya ce idan adalci ake so mulkin Najeriya ya kamata ta koma kudancin Najeriya a 2023.

Kamar yadda Channels Television ta rahoto, gwamnan na Benue ya bayyana hakan ne a filin wasa na Adokiye Amiesimaka lokacin kaddamar da kamfen din PDP a Fatakwal a jihar Rivers.

Ortom yana daya daga cikin gwamnonin G-5 wadanda suka sako jam'iyyar PDP a gaba kan cewa sai ta mika shugabancin jam'iyyar ga kudu kafin su goyi bayan Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel