Babban Bankin Kasa CBN Ya Hana Cire Sabbin Kudi Akan Kanta Sai Dai A ATM kawai

Babban Bankin Kasa CBN Ya Hana Cire Sabbin Kudi Akan Kanta Sai Dai A ATM kawai

  • Wa'adin daina amfani da tsoffin kudi yan N200, N500 da kuma N100 zai zo ne akarshen watan nan wato 29 ga watan Janairu
  • Tsarin sauya kudin dai ya bar baya da kura inda masana da dama da yan kasa ke sukar lamirin al'amarin
  • Bankin dai yace ya fitar da wannan tsarin ne dan magance yadda ake satar kudin kasa da kuma yadda ake biya kudaden kuma basa zagaya a tsakanin al'umma

Abuja - Babban bankin kasa CBN, ya umarci bankunan kasuwancin kasar nan da su daina bayar da sabbin kudade akan kanta, sai dai a injinun cirar kudi na ATM.

Dakar sannan ta kara jaddadawa bankunan kan su kiyaye da umarnin tare da aiwatar da shi a hada-hadar kudi.

yayin da yake bayyanawa wakilin jaridar The Cable, mai magana da yawun Osita Nwasinobi yace dokar ta fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Kungiyar Kafa Kasar Yarbawa Adeniran Ya Yi Murabus, Ya Bada Dalili

Yace hukumomin gudanarwar bankin sun gano cewa akwai korafe-korafe daga yan Nigeria kan yadda sabbin kudin suka ki zagayawa a tsakaninsu, alhalin sun kusan kwana ashirin da sakinsu.

Mai magana da yawun bankin ya ce dokar an bayar da ita ne dan kara sakin kudin da kuma kara yawan zagaya kudin kafin wa'adin kare amfani da tsoffin yayi a ranar 29 ga wannan watan.

Mai magan da yawun bankin yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Wannan dokar muna da tabbacin cewa zai taimaka wajen magance karancin kudin a tsakanin yan kasa"

Munji Korafin Yan Kasa

Mai magana da yawun bankin yace muji korafin yan kasa kan batutuwan da suke yi na cewa karancin sabbin kudaden a bankuna da hannun mutane.

Dan haka muka umarci manyan bankunan Nigeria na kasuwancin da su saki kudaden kuma su daina bayar da su akan kanta sai dai a ATM

Kara karanta wannan

Ko Tinubu Yana Taba Kirifto Ne: Yasha Alwashin Taimakon Yan Kirifto In Ya Kai Ga Gaci

"Hakan Zai taimaka wajen yaduwa kudin a tsakanin al'ummar"

An yi kira da jama'a suyi hankali da zagayawar kudaden jabu a tsakanin al'umma

Babban bankin kasa da hukumar tsaron Nigeria sunyi kira al'umma da suyi hattara da yadda kudaden jabu suke yawo a tsakanin al'umma.

Sabbin kudin dai basu zo da wani farin jini ba, sabida yadda al'umma suka ki kudin kuma suke kin karbarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel