Bayan Canjawa Ƙudin Nigeria Fasali Da CBN, Yayi, Jabun Kudi Sun Fara Tumbuɗi A Tsakanin Al'umma

Bayan Canjawa Ƙudin Nigeria Fasali Da CBN, Yayi, Jabun Kudi Sun Fara Tumbuɗi A Tsakanin Al'umma

  • Akwai kokwanto tun tuni a zukatan mutane kan yadda za'a sha fama wajen babbance wannan kudin da kuma na Jabu.
  • Legit.ng Hausa ta fitar da wani rahoto bayan kallar wani bidiyo na wata mata data ki karbar sabbin kudin tana mai cewa na jabu ne.
  • Wanne tanadi babban bankin kasa CBN da gwamnan bankin sukai dan ganin an shawo kan matsalar jabun kudi a tsakanin al'umma.

Kwanaki kadan da fara zagawar sabbin kudin da babban bankin kasa ya sakewa fasali, an samu kwararar jabu N1000 a hannun mutane. Rahotan Vangaurd

A wani fefan bidiyo an ga yadda wani abokin cinikaiyyar wata mata mai sana'ar POS, yaje yin mu'amalar banki a wajen amma yake kokarin nu na mata banbancin kudin gaske da na jabun.

Kara karanta wannan

Wata Mata Tace Allah-Fa-Fir Bazata Karbi Sabon Kudi Ba, Sabida Jabu Ne

A nuna mata kai tsaye cewa wannan shine jabun, yayin da ya nuna mata wannan sune na gaske.

NewNaira
Bayan Canjawa Ƙudin Nigeria Fasali Da CBN, Yayi, Jabun Kudi Sun Fara Tumbuɗi A Tsakanin Al'umma Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa kudin na gaske yana da wani tambarin mai ratsin kalar gwal a gefen kudin daga dama, sannan tambarin ko kayi ƙoƙarin gogeshi bazai gogu ba.

Amma shi tsohon kudin da aka canja baida irin wannan tambarin daga kasan wajen da gwamnan babban banki ya sawa hannu.

In za'a iya tunawa CBN, a sake sabbin kudin da ya canjawa fasali a ranar 15 ga watan Disambar wannan shekarar

Amma har yanzu bankuna na bawa mutane tsoffin kudin, suna masu cewa sabbin ne basu wadata a hannunsu ba, dan haka basu da wata hanya illa su bayar da taoffin.

Mutane Sunki Sakin Jiki Da Sabbin Kudi.

Kara karanta wannan

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

A wani faifen bidiyo da wata mata ke sai da abinci ya bazu, anga matar na kin karbar kudi daga abokin cinikaiyyarta sabida zargin cewa kudin na Jabu ne ba gaske bane.

Hhaka nan ma a wani bidiyon da wata mai amfani da Tik-tok mai suna Mama ta wallafa shima an ga wani mai sai da kayan marmari ki. karbar sabbin kudin yana mai cewa shi bai waye da su ba.

Matsalar Canjin Kudi dai daga masana na ganin ba'a dauki hanyar da kamata ace an bi dan kaddamar da ita . Dr. Yusuf Moda na cikin wanda suke da wannan tinanin

.

Asali: Legit.ng

Online view pixel