FG ta Kori Sama da Ma'aikata 500 da Aka Dauka ba Bisa Ka'ida ba a Ma'aikatar Kwadago

FG ta Kori Sama da Ma'aikata 500 da Aka Dauka ba Bisa Ka'ida ba a Ma'aikatar Kwadago

  • Gwamnatin tarayya ta kori ma'aikata sama da 500 da ka dauka a ma'aikatar kwadago da ayyuka ba bisa ka'ida ba
  • Kamar yadda bincike ya bayyana, an dauki ma'aikatan makwanni kafin zaben shekarar 2019 ba tare da sanin ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ba
  • Wata majiya ta bayyana yadda korarrun ma'aikatan suka bada cin hancin N300,000 kowannensu kafin basu gurbin aikin, sannan ba a biyasu ko ficika ba tun daga lokacin da suka fara aiki

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kori sama da ma'aikatan da ka dauka ba bisa ka'ida ba 500 a ma'aikatar aiki da kwadago ta tarayya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Abuja
FG ta Kori Sama da Ma'aikata 500 da Aka Dauka ba Bisa Ka'ida ba a Ma'aikatar Kwadago. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An gano yadda aka daukesu aiki a cikin ma'aikatar makwanni kafin zaben 2019 - amma ba tare da sanin ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ba.

Kara karanta wannan

Rudani: Majinyata sun rude, gobara ta kama a babban asibitin kwararrun jihar Arewa

Kamar yadda takardar cikin gida da Hussain Abdulrahman, daraktan kula da kayan al'umma, ya rattaba, wanda The Cable ta samu, an kori "korarrun ma'aikatan" ne saboda yadda kwamitin taki sanya su a tsarin biyan kudi na (IPPIS).

Abdulrahman ya bayyana a takardar yadda aka ki bin dokar shugaban ma'aikatan gwamnatin da ma'aikatar kwadagon tayi yayin daukar aikin ya zama musabbabin korar ma'aikatan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, takardar ta umarci ma'aikatan da su maidowa gwamnati dukkan mallakinta dake hannunsu ga shugabanninsu na aiki.

"Tare da dogara da takardar daga shugaban ma'aikatan tarayya mai lambar shaida . NCSF/CMO)IPPIS/S.2/VOLT da ta fita ranar 5 ga watan Satumba, 2022, game da batun dake sama, in umarce ni da in sanar da jerin sunayen mutanen da kwamitin kaddamar da sabbin ma'aikata cikin tsarin biyan albashi na IPPIS cewa ba a shigar da su tsarin ba."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda aka Tarwatsa Bikin Aure Kan Maggi da Kiret din Maltina da Dangin Miji Basu Kai Wurin Daurin Aure ba

- Kamar yadda takardar ta bayyana.

"Haka zalika, an dauki ma'aikatan ne ba tare da izini daga ofishin ta ba. An bukaci dukkan wadanda lamarin ya shafa da su maido da duk wani abu mallakin gwamnati dake hannunsu ga shugabanninsu."

Wata babbar majiya a ma'aikatar - wanda ba ya bukatar a ambaci sunansa saboda tsoron cin zarafi - ya bayyanawa The Cable yadda ma'aikatan suka biya kudi don a basu aikin.

Siyan gurbin aiki, musamman na gwamati, ba sabon abu bane a tsarin aikin gwamnati.

Majiyar ta kara da bayyana yadda ma'aikatar ta dauki ma'aikatan da aka kora a 2019, inda ya kara da cewa, yayin da aka ba wasu lambobin IPPIS da mukamai, wasu ba a basu ba.

Wadanda ba a ba Lambobin IPPIS ba sune wadanda ba a biya ba tun lokacin.

Haka zalika, wata majiya ta kara da cewa:

"Sun siyar da gurbin aikin da salahan bayi a 2019. Wadannan mutane tun daga lokacin ba a biya su ba har yau. Za ka gansu sun yi zaune cikin ma'aikatar. Abun da muka sani shi ne, tabbas wannan gwaramar na tsakanin tsohon sakataren dindindin, Alo da Ake Adeniyi."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Hedkwatar 'Yan Sanda, Sun Tashi Bama-Bamai

- A cewar majiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng