Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Ta'adda, Sun Sheke Daya, Sun Ceto Mutane A Katsina

Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Ta'adda, Sun Sheke Daya, Sun Ceto Mutane A Katsina

  • Yan sanda a jihar Katsina sun yi nasarar fatattakar yan ta'adda da suka kai hari kauyen Karfi, karamar hukumar Malumfashi
  • Bayan musayar wuta, yan sandan sun kashe dan ta'adda guda sun kuma ceto wani mutum da aka sace shi daga garin
  • Kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce rundunar za ta bada karin bayani idan an kammala bincike kan lamarin

Jihar Katsina - Yan sandan jihar Katsina sun ce sun dakile wani hari da yan ta'adda suka kawo kuma sun ceto wani da aka sace aka yi garkuwa da shi, Channels TV ta rahoto.

Yayin da ya ke magana kan harin, kakakin yan sanda Gambo Isah ya ce rundunar ta yi nasarar halaka daya cikin yan sandan tare da ceto wanda aka sace, ba tare da an masa lahani ba.

Kara karanta wannan

Ba zama: Legas ta rikici, direba ya banke dan sanda ya fece, runduna ta fusata

Taswirar Katsina
Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Ta'adda, Sun Sheke Daya, Sun Ceto Mutane A Katsina. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da rana, bayan rundunar ta samu kiran neman dauki da ke cewa yan ta'adda masu yawa, suna harbi da AK-47, sun kutsa gidan wani Kabir Sule, dan shekara 37 a kauyen Karfi, karamar hukumar Malumfashi.

A cewar bayanan da aka samu, maharan sun sace Sule bayan harin.

DPO na yan sanda a Malumfashi, ya jagoranci tawagar yan sanda da yan bijilante zuwa yankin inda suka yi musayar wuta da yan ta'addan, rahoton AIT.

Daga bisani yan ta'addan sun tsere da rauni, an kuma gano gawar wasu maharan da ta yi wu sun mutu sakamakon raunin da aka musu.

A cewar SP Gambo, za a fitar da karin bayani kan abin da ya farun a nan gaba idan an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Daga Jin Dumi Ashe Karshensu Ne Yazo, Yadda Wasu yan gida suka rasa ransu

Wani mazaunin Abuja ya halaka abokinsa ya birne gawarsa saboda rikici kan kudi

Yan sanda sun kama wani mutum dan shekara 63 mazaunin Abuja, Taiwo Ojo, kan zarginsa da halaka abokinsa mai suna Philip Kura.

Rahotanni sun bayyana cewa Ojo ya buga wa Philip shebur ne a kansa yayin da suke jayayya kan wani kudi sannan ya janye gawarsa ya boye a cikin wani dan karamin daji, daga bisani ya birne.

Kamar yadda The Punch ta rahoto, Ojo ya aikata wannan mummunan lamari ne a ranar 23 ga watan Disamba kamar yadda majiya ta bayanan sirri ta nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel