Abun Bakin Ciki: Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano

Abun Bakin Ciki: Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano

  • Wani magidanci mai suna Sulaiman Idris da amaryarsa, Maimuna Halliru, sun hadu da ajalinsu lokaci guda a jihar Kano
  • Ma'auratan sun rasa ransu sakamakon hayakin garwashi da ya turnuke dakinsu suna tsaka da bacci
  • Kamar yadda rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana, sun kunna garwashi domin dumama daki sakamakon sanyi da ake yi amma sai aka hadu da bacin rana

Kano - Wani mummunan al'amari ya riski al'ummar kauyen Kwa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano yayin da wasu ma'aurata, Sulaiman Idris mai shekaru 28 da matarsa Maimuna Halliru, mai shekaru 20 suka mutu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an tsinci ma'auratan ne kwance babu rai a kan gadonsu na sunnah.

Jihar Kano
Abun Bakin Ciki: Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano Hoto: The Nation
Asali: UGC

An tattaro cewa ma'auratan sun kunna garwashi domin dumama dakinsu sakamakon yanayi na sanyi da ake ciki kuma a haka ne hayaki ya turnuke su yayin da suke cikin bacci.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Dan Sanda Ya Kashe Matasa 2 Tare Da Jikkata Wasu 3 a Wata Jahar Arewa

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya ce kakar mijin ta lura da rashin jin motsi daga bangaren ma'auratan don haka ta fasa kofar dakinsu inda ta gansu kwance magashiyan a kan gadonsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SP Haruna ya ce an kwashi ma'auratan zuwa asibitin Muratala Mohammed da ke Kano inda likita ya tabbatar da mutuwarsu, rahoton PM News.

A cewarsa:

"A ranar 3 ga watan Janairun 2023 da misalin 2100hrs, an samu wani rahoto daga kauyen Kwa, karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano cewa an lura wasu ma'aurata, Sulaiman Idris mai shekaru 28 da Maimuna Halliru mai shekaru 20 basu fito daga dakin aurensu ba tun a ranar 02/01/2023 da misalin 2300hrs. Da kakar mijin ta fasa kofar dakinsu, sai ta ga ma'auratan kwance a kan gadonsu basa motsi, da kaurin hayaki a dakinsu.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

"Da samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya umurci wata tawaga karkashin jagorancin CSP Ahmed Hamza, DPO na yankin Dawakin Rofa da su isa wajen. An kwashi mutanen daga wajen sannan aka kai su asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano inda likita ya tabbatar da mutuwar ma'auratan.
"Da fara bincike, an gano cewa mamatan sun kunna garwashi don dumama dakinsu saboda sanyi, sannan suka rufe koina lamarin da ya sa hayaki ya turnuke koina yayin da suke bacci. Sai dai, ana ci gaba da bincike.
"Kwamishinan yan sanda, ya shawarci al'ummar jihar Kano kan bukatar yin taka-tsan-tsan yayin amfani da wuta da lantarki da daukar matakan kare kai a wannan lokaci na sanyi wanda ke da matukar hatsari na afkuwar gobara."

An gano asibitoci da shagunan magunguna 130 da likitocin bogi suka bude a Kano

A wani labarin kuma, wani kwamiti a karamar hukumar Tudun Wada a Kano, ya ce sun gano asibitoci da shagunan sayar da magunguna 130 da likitocin bogi suka bude kuma suke gudanar da aiki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng