Kebbi: Manoma 10 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Jirgin Ruwa ya Nitse

Kebbi: Manoma 10 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Jirgin Ruwa ya Nitse

  • A kalla rayukan mutane goma sun salwanta sanadiyyar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Koka ta jihar Kebbi
  • An ruwaito yadda lamarin ya auku ranar Talata, inda jirgin ruwan ya kife da fasinjoji sama da 100, yayin da aka ceto sama da kashi 80
  • An gano yadda jrigin ke dauke da kusan duka matasa, sai dai an ciro gawawwakin mata 4 da maza 6, yayin da har yanzu ake cigaba da neman sauran

Kebbi - An ruwaito yadda mutane goma suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a kananan hukumomin Koko/Nesse na jihar Kebbi a ranar Talata, jaridar TheCable ta rahoto.

Taswirar Kebbi
Kebbi: Manoma 10 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Jirgin Ruwa ya Nitse. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda NAN ta bayyana cewa, Yahaya Bello, shugaban karamar hukumar Koko yayi bayanin yadda lamarin ya kasance.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

A cewar Bello, jirgin ruwan dake dauke da sama da fasinjoji 100 wadanda manoman shinkafa ne a Samanaji, wata fadama, ya tafka hatsari, Daily Trust ta rahoto.

Ya kara da cewa, an gano gawawwakin mata hudu da maza shida, inda ya bayyana yadda aka ceto kashi 80 na fasinjojin yayin da har yanzu ba a ga sauran ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kusan duk fasinjojin matasa ne; kananan yara maza da mata. Mun gano gawawwakin mata hudu da maza shida.
"Mun ceto sama da kashi 80 na fasinjojin, yayin da muke cigaba da neman sauran.
"Kafin aukuwar lamarin, mun shirya taron gaggawa da hakimin Dutsin Mari da sauran sarakuna da shugabannin matuka jirgin ruwan yankin.
"Ganawar don wayar musu da kai gami da jan kunnensu game da amfani da kaya masu matsanantancin nauyi, tsoffin jiragen ruwa, zuba kaya da yawa da kuma tafiyar dare ne aka yi."

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Dan Sanda Ya Kashe Matasa 2 Tare Da Jikkata Wasu 3 a Wata Jahar Arewa

- Yace.

A cewarsa, ana iya kokarin ganin an tseratar da sauran wadanda lamarin ya auku dasu, inda ya kara da cewa kungiyar da farko ta raba sabbin jiragen ruwa 20 don gudun nitsewa.

Haka zalika, Nafiu Abubakar, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Hatsarin mota yayi ajalin mutum 18 a Bauchi

A wani labari na daban, mummunan hatsarin mota da ya auku a kauyen Nabardo dake jihar Bauchi ya lakume rayukan mutum 18.

An gano cewa, fasinjojin sun kone ne ta yadda ba a iya gane ko daya daga cikinsu a ranar Laraba da yammaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel