Mutum 15 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata A Mummunan Hadarin Mota Da Ya Faru A Shahararriyar Jihar Arewa

Mutum 15 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata A Mummunan Hadarin Mota Da Ya Faru A Shahararriyar Jihar Arewa

  • Allah ya yi wa wasu fasinjoji 15 rasuwa sakamakon hatsarin mota a Koton-Karfe da ke babban hanyan Lokoja-Abuja, jihar Kogi
  • Kwamandan FRSC ya bayyana cewa bin hanyar da ta tasa ba da direban bas din ya yi ne ya janyo hatsarin
  • Tuni dai an kwashe gawar wadanda suka rasu an kai FMC Lokoja yayin da wadanda suka jikkata suna wani asibitin ana musu magani

Jihar Kogi - Hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, a ranar Talata ta tabbatar cewa mutane 15 sun mutu, wasu biyar sun jikkata sakamakon hadarin mota da ya faru a Kogi, Daily Trust ta rahoto.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta rahoto cewa hadarin ya faru ne bayan karo da wata J-5 da Tankan Man Fetur suka yi a Koton-Karfe da ke babban hanyan Lokoja-Abuja misalin karfe 7.30 na safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Kaico: Tashin hankali yayin da mai siyar da fetur ya babbake abokinsa a kan cajar waya

FRSC Nigeria
Mutum 15 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata A Hatsarin Mota Da Ya Faru A Shahararriyar Jihar Arewa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamandan hukumar, Stephen Dawulung, Sekta Kwamanda na Kogi, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an garzaya da mutane biyar din da suka yi rauni zuwa asibitin Ideal a Koton Karfe nan take don basu kulawa.

Dawulung ya ce an kai gawarwakin wadanda suka rasu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Lokoja, Guardian ta kara.

Kwamandan FRSC ya bayyana sababin hatsarin motan

Kwamandan ya yi bayanin cewa rashin bin dokokin hanya ne da direban bas din ya yi, ya janyo hatsarin don ba hanyarsa ya bi ba.

Ya ce:

"Direban bas din ya bar hanyarsa yana tuki a ta 'one way' kuma yana gudu hakan yasa ya yi karo da tankar man fetur da ke tahowa.
"Mun gode Allah tankar man fetur din bata kama da wuta ba, da abin ya fi haka muni.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

"Abin bakin cikin shine bas din ta dauke karafa tare da fasinjoji 17, 15 cikinsu sun rasu sakamakon karon da motoccin suka yi."

Daga karshe ya yi kira ga direbobi su rika kiyayye dokokin hanya tare da kulawa da lafiyar ababen hawansu don kiyayye afkuwar hakan a gaba.

Mutane 19 sun kone kurmus sakamakon mummunan hadarin mota a birnin tarayya Abuja

A wani rahoton, Hukumar kiyayye haddura na kasa ta tabbatar da mutuwar mutane 19 a wani hadarin mota da ya faru a Yanhoji zuwa Gwagwalada a Abuja.

Dauda Biu, mukadashin shugaban FRSC na Abuja ne tabbatar da hakan yayin da ya ziyarci wurin da abin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel