Mutum 19 Sun Kone Kurmus A Mumunan Hadarin Mota a Abuja

Mutum 19 Sun Kone Kurmus A Mumunan Hadarin Mota a Abuja

  • Mutum 19 sun kone kurmus yayinda motoci uku suka ci karo da juna a birnin tarayya Abuja
  • Cikin Mutum 31 da hadarin ya shafa, an garzaya da sauran mutum takwas da suka jigata asibiti
  • Shugaban hukumar kiyaye hadura ya yi kira da direbobi su daina tuki da dare kuma su daina gudu

Gwagwalada - An tabbatar da mutuwan mutum goma sha tara (19) sakamakon mumunan hadarin da ya auku a babban titin Yangoji-Gwagwalada dake birnin tarayya Abuja.

Wannan hadari ya auku ne da cikin daren Lahadi, 18 ga Satumba, 2022.

Mukaddashin shugaban hukumar kiyaye hadura na tarayya, Dauda Biu, ya tabbatar da hakan a ziyarar da ya kai wajen, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

FRSC.
Mutum 19 Sun Kone Kurmus A Mumunan Hadarin Mota a Abuja
Asali: Facebook

Dauda Biu yace hadarin ya auku ne tsakanin motoci uku - Toyota Hiace Biyu da mota Citroen.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Daga cikin mutum 31 da hadarin ya rutsa da su akwai maza bakwai da mace daya da suka jigata sosai, yayinda 19 suka kone kurmus ko ganesu ba za'a iya ba."
"Bincike ya nuna cewa babban musababbin hadarin gudu ne da kuma kokarin wuce juna."
"Motar Toyota Hiace mai lamba MUB- 30 LG, ta buge motar Citreon kawai sai ta kama da wuta kuma dukkan wadanda ke ciki suka mutu."
"Ita kuma motar ta biyu ta buge ta farko daga baya itama ta kama da wuta."

Ya kara da cewa hukumar yan sanda ta tattauna da masu ruwa da tsaki don birne gawawwaki 18 don ba za'a iya ajiyesu don gano iyalansu saboda sun kone kurmus.

Wadanda suka jigata kuwa an garzaya da su wani asibiti dake Kwali, yayinda aka ajiye gawa daya da bata kone sosai ba a dakin ajiye gagwwakin asibitin General na Kwali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel