Gobara Ta Kone Dakin Gwaje-Gwaje Na Asibitin Kwararrun Jihar Filato
- Rahotanni da muke samu daga jihar Filato sun bayyana yadda wani yanki na asibitin kwararru a jihar ya kama da wuta
- An ce an yi asarar kayayyakin aiki na miliyoyi a lokacin da wutar ta kama cikin dare, yayin da babu ma'aikata da yawa a ciki
- Sai dai, an yi sa'a a ba a samu asarar rai ba, hukumar asibiti ta tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda aka tattaro
Jos, Filato - Gobara ta kama a dakin gwaje-waje na asibitin kwararre da ke Jos a jihar Filato da sanyin safiyar jiya Talata 3 ga watan Janairun 2023.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa, wannan mummunan gobara ta yi sanadiyyar asarar kadarori masu matukar daraja da suka kai miliyoyin Nairori.
An ce wutar ta kama ne a lokacin da ma’aikatan aikin dare ne kadai suke cikin asibitin, amma ba a rasa rai ba.
An tattaro cewa, an gano tashin wutar ne da misalin karfe 2 na dare kuma ba a iya shawo kanta ba kasancewar majinyatan da suka tsorata sun tada hankali a asibitin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kayayyakin aikin asibiti, kayan aikin ofis da sauran abubuwa masu darajan miliyoyi ne suka kone a lokacin da wutar ke ci.
Hukumar asibiti ta tabbatar da faruwar lamarin
Kakakin asibitin, Talatu Angi ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana cewa:
“Mun zo da safen nan (jiya) sai muka ga wurin ya kone amma an yi sa’a dakin gwaje-gwajen ne kadai kasancewar wutar bata bazu zuwa wani bangare ba.
“Ba a rasa rai ba, wutar tana da yawa kuma ta fi karfin tulun kashe wuta da ake dashi.”
Ya zuwa yanzu, rahoton AIT ya ce, hukumar kashe gobara ta jihar ta yi nasarar kashe gobarar.
Ana yawan samun tashin gobara a ofisoshin gwamnati a Najeriya, musamman a shekarar da ta gabata.
Gobara ta Lamushe Rayukan Yara 2 Dake Garkame a Cikin Daki
A wani labarin kuma, gobara ta ci wasu yara biyu a cikin gidansu da jihar Imo, lamarin da ya jawo jimami.
An ruwaito cewa, gobarar ta kama ne bayan da mahaifiyar ta rufe yaran a daki ta fita zuwa gidan makwabta
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana yadda mahaifiyar ta rufe yaran masu kananan shekaru a gida.
Asali: Legit.ng