Sojan Fadar Shugaban Kasa Ya Bude Wuta, Ya Yi Sanadiyyar Rasa Rai a Abuja

Sojan Fadar Shugaban Kasa Ya Bude Wuta, Ya Yi Sanadiyyar Rasa Rai a Abuja

  • Ana zargin wani soja mai suna Abubakar Idris ya kashe wani Bawan Allah a kan titi a birnin Abuja
  • Wannan mutumi da aka hallaka ya na kan babur din ‘dan acaba ne sai suka ci karo da sojoji su na aiki
  • Mazauna yankin sun ce sojan ne ya harbe fasinjan, nan-take kowa ya watse aka bar gawarsa a hanya

Abuja - Wani jami’in sojan Najeriya da ke aiki da dogaran fadar shugaban kasa, Abubakar Idris, ya budewa mutane wuta a titi a birnin tarayya Abuja.

Rahoton da muka samu daga Punch ranar Talata 3 ga watan Junairu 2022 ya tabbatar da sojan ya aika wani fasinjan babur zuwa barzahu nan-take.

Wannan lamari mai ban takaici dai ya faru ne kusan karfe 1:00 na tsakar dare a gab da wata gada a kan titin Jonathan Aguiyi Ironsi a unguwar Asokoro.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

Majiya ta shaidawa jaridar an dauki wanda aka harban zuwa asibitin yankin Asokoro a Abuja domin kwararru su yi bincike a kan dalilin mutuwar.

Shaida daga bakin wata majiya

“Abin takaici ne. jami’an sojojin kasar su na bakin aiki a daren (Lahadi/Litinin) sai Abubakar Idris ya hango wasu matuka babur su na zuwa kusa da su a gadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in (Idris) ya na kokarin tsaida daya daga cikin masu babur din da yake dauke da fasinja, ana haka sai buda masu wuta, nan take sai ya hallaka fasinjan.
Shi kuma ‘dan acaban da sauran matuka baburan suka tsere.”

- Majiya

Sojan Najeriya
Wani soja yana bakin aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

"A nan sojoji suka bar gawarsa"

A wani kaulin kuma, wani wanda ya san yadda abin ya faru, ya bayyana cewa sojojin sun tsere sun bar gawan wannan mutumi, sai da ‘yan sanda suka zo.

Kara karanta wannan

Ashe babu dadi: Kasurgumin dan bindiga ya firgita, an rusa gidansa, an kashe yaransa 16

Idan abin da wata majiyar ta fada gaskiya ne, a kan titi sojojin suka bar gawar har sai kusan karfe 3:00 na dare da ‘yan sanda suka zo, aka kai gawar asibiti.

Ba mu san an yi ba - Sojoji

Sahara Reporters ta ce Mai magana da yawun bakin dakarun sojojin, Abakpa Godfrey ya fadawa ‘yan jarida bai san da labarin wannan abin da ya auku ba.

Godfrey ya ce sa’ilin da ake tunanin abin ya faru, ya samu izinin barin Abuja, saboda haka ba zai iya furta komai da molon kai daga dawowansa bakin aiki ba.

Karshen 'Yan G5 ya zo - Dino

A bangaren siyasa, an ji labari Sanata Dino Melaye ya fito yana cewa duk ‘Yan Jam’iyyar PDP har ‘Yan APC za su zabi Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa ya ce idan Gwamnonin G5 suka ki goyon bayan 'dan takaran PDP a babban zabe, kashinsu ya bushe a siyasa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Wanda Yake Goyon Baya Ya Gaji Buhari a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng