Jerin Kasashe 64 da Najeriya Ta Shigo da Man Fetur Dinsu Yayin da NNPC Ta Siya Man N1.2trn a Cikin Wata 3
- Wani sabon rahoto ya bayyana cewa, kamfanin man fetur na Najeriy ya kashe sama da N1.2trn wajen shigo da man fetur a watanni uku kacal
- An shigo da wannan man fetur ne daga kasashen waje da suka hada da jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya
- A ‘yan kwanakin baya da suka wuce, ‘yan Najeriya sun shaida tsada da karancin man fetur a gidajen man kusan dukkan sassan kasar
Hukumar kididdiga ta NBS ta bayyana cewa, Najeriya ta kashe N1.199trn wajen shigo da man fetur a cikin watanni uku na tsakiyar shekarar da ta gabata; 2022 (tsakanin Yuli zuwa Satumba)
NBS ta bayyana hakan ne a cikin kididdigar harkalla da kasashen waje da Najeriya ta yi a kwata na uku na shekarar 2022 da ta kare, kamar yadda Legit.ng ta tattaro a shafin hukumar na yanar gizo.
A cewar rahoton, kudaden da aka kashe wajen shigo da mai tsakanin Yuli da Satumban bara ya kai karin 16.2% idan aka kwatanta da N1.026trn na kudaden da aka siyo irin wadannan kaya a shekarar 2021.
NBS ta kuma bayyana cewa, kudurin kwata na uku na 2022 na shigo da man fetur ya kasance mafi girma a ‘yan shekarun da suka gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A irin wadannan kwata na uku a shekarun 2018, 2019 da 2020, an kashe N883.565bn, N371.8bn da N532.615bn bi da bi na shigo da man fetur.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ne kadai ke shigo da man fetur daga wasu kasashen waje a Najeriya.
Kayayyakin da aka fi shigo dasu Najeriya
Gaba dayan kayayyakin waje da Najeriya ta shigo dasu a kwata na uku a 2022 sun kai na jumillar kudade N5.66trn.
NBS ta bayyana cewa, man fetur ne a kan gaba a jerin kayayyakin da aka shigo dasu Najeriya a cikin wadancan watanni uku, daga shi sai man gas da aka shigo da na N261.595.
Alkama kuwa ta cinye N252.621bn, kuma itace ta uku daga jerin kayayyakin da aka shigo dasu Najeriya watannin uku.
Jerin kasashen da aka shigo da man fetur daga garesu
NBS bata bayyana daga wasu kasashe ne Najeriya ta shigo da man fetur ba, amma wani rahoton WITS ya nuna kasashen da Najeriya ke harkallar man fetur dasu kamar haka:
- United Arab Emirates
- Austria
- Belgium
- Benin
- Bulgaria
- Canada
- Switzerland
- Chile
- China
- Cote d'Ivoire
- Germany
- Denmark
- Egypt, Arab Rep.
- Spain
- Estonia
- Ethiopia(excludes Eritrea)
- Finland
- France
- Gabon
- United Kingdom
- Ghana
- Guinea
- Equatorial Guinea
- Greece
- Hungary
- Indonesia
- India
- Ireland
- Iraq
- Israel
- Italy
- Japan
- Korea, Rep.
- Kuwait
- Lebanon
- Sri Lanka
- Lithuania
- Luxembourg
- Latvia
- Morocco
- Mexico
- Malaysia
- Niger
- Nicaragua
- Netherlands
- Norway
- Other Asia, nes
- Pakistan
- Poland
- Korea, Dem. Rep.
- Portugal
- Romania
- Russian Federation
- Saudi Arabia
- Singapore
- Sweden
- Eswatini
- Togo
- Thailand
- Tunisia
- Turkey
- United States
- Vietnam
- South Africa
A kullum gwamnatin Najeriya na bayyana yunkurin dakile wahalar mam fetur a kasar, amma abin bai kai wa ga nasara.
Asali: Legit.ng