Sabuwar Mota: Hazikin Dan Najeriya Ya Kera Motar G-Wagon Ya Kuma Tuka Ta a Cikin Gari, Bidiyon Ya Yadu

Sabuwar Mota: Hazikin Dan Najeriya Ya Kera Motar G-Wagon Ya Kuma Tuka Ta a Cikin Gari, Bidiyon Ya Yadu

  • An gano wani hazikin dan Najeriya yana tuka motar G-Wagon wanda ya kera da hannunsa a cikin gari
  • A wani bidiyon TikTok da Kingsley Reigns Idoko ya wallafa, an gano yaron yana tuka motar a harabar cikin gida yayin da ahlinsa ke jinjina masa
  • Masu amfani da TikTok na ta jinjinawa matashin yaron sannan wasu na kira ga a bashi tallafi

Jama'a a soshiyal midiya sun jinjinawa wani matashin yaro da ya kera motar G-Wagon bayan cin karo da wani bidiyo a TikTok.

Wani mai amfani da TikTok, Kingsley Reigns Idoko, shine ya wallafa bidiyon a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba kuma ya nuno yaron yana tuka motar a cikin gari.

Motar G-wagon
Sabuwar Mota: Hazikin Dan Najeriya Ya Kera Motar G-Wagon Ya Kuma Tuka Ta a Cikin Gari, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@kingsleyreignsidoko.
Asali: UGC

Matashin yaron ya tuka motar G-Wagon din a harabar gidansu kuma danginsa suna ta jinjina masa a kan wannan fasaharsa.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi

Dan Najeriya da ya kera motar G-Wagon

Motar da aka yiwa bakin fenti kuma ya yi kama da G-Wagon tana ta juyawa ba tare da wata matsala ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kingsley ya ce matashin kaninsa ne amma ya gaza bayanin yadda aka yi ya kera motar.

Ya rubuta a jikin bidiyon:

"Kanina ya kera wata motar G-Wagon dan Allah ku tayani yada shi."

Masu amfani da TikTok sun yabama yaron a kan wannan kokari nasa. Da dama sun yi kira ga a tallafawa mutane da suka nuna iyawarsu irin haka a bangaren fasaha.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user7007593736174Episode ya ce:

"Mugun ido ba zai taba ganinka Amin...Allah ya kara daukaka dan uwa."

@gilberttimothy301 ya yi martani:

"Ma shaa Allah! Allah ya kara daukaka dan uwa."

@Anthony moris ya yi martani:

"Kana da makoma mai kyau."

Kara karanta wannan

Ta tabo inda yake so: Amarya ta shafa kirjin ango a wurin biki, ya cika mata jaka da daloli

@Sammy ya ce:

"Abu ya yi kyau! Amma dan Allah jire logon Toyotan nan sannan ka saka naka logon."

@user37531645809204 ya yi martani:

"Ina son sanin gayen nan."

@Maskman ya ce:

"Ya nemi nashi logon mai kyau da kansa, amfani da logon Benz kamar sadaukar da nasarar shi gare su ne."

Dalibin Jami'a Ya Kirkiri Motar Daukar Kaya a Matsayin 'Project' Dinsa

A wani labarin, wani dalibin jami'ar Benin ya kera wata motar daukar kaya a matsayin 'project' dinsa na jami'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel