Luguden Wutan Sojojin Sama Ya Kai Ga Kashe Manyan Mayakan Boko Haram a Jihar Borno
- Luguden wutan da sojin saman Najeriya suka yi ya kai ga kashe wasu manyan sojojin Boko Haram/ISWAP
- An ruwaito cewa, an jikkata wasu ‘yan ta’adda da yawa a hare-haren da aka kai a karshen watan Disamba
- Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’addan kasar nan, musamman a shekarar nan
Bama, jihar Borno - Luguden wuta da rundunar sojin sama karkashin Operation Hadin kai suka yi ya kai ga mutuwar manyan mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Wannan farmakin da sojoji suka kai kan wasu wuraren da ‘yan ta’addan ke buya ya yiwa 'yan Boko Haram barna, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.
An naqalto cewa, harin na soji a jajiberin Kirsimeti da kuma ranar Talatar da ta gabata ya kai ga hallaka ‘yan ta’adda a yankunan Sheutari da Mantari a Lawanti/Mallam Mastari/ Abbaram duk a gundunwar Bama.
An ruwaito cewa, yankunan Sheutari da Mantari suna karkashin ‘yan ta’addan da suka addabi jama’a a dajin Sambisa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ce ta gano cewa, wadanda luguden wutan soji ya rutsa da su wasu manyan sojojin yakin Boko Haram, wasu sun mutu wasu kuma sun tsira da munanan raunuka.
'Yan ta'adda sun tsere, an yiwa wasu jinya
A bangare guda, wani kwararren mai sharhi da bincike kan lamarin tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya, Zagazola Makama ya ce an yiwa ‘yan ta’adda da suka ji raunin jinya a yammacin Mantari; kasa da tazarar mita 500.
Ya kara da cewa, majiyoyin sirri na tsaro sun tattaro cewa, aikin sojin ya kai ga yankin Shehutari, inda ‘yan ta’adda da dama suka gamu da ajalinsu.
An raunata da yawa, wasu kuma sun gudu sun buya cikin manyan bishiyoyin da ke cikin kungurmin dajin yankin.
Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira
A watan Oktoba, yaki mai tsanani ya barke tsakanin 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP a jihar Bono.
Wannan lamari ya kai ga mutuwar manyan 'yan ta'addan, kamar yadda rahotannin tsaro daga yankin suka bayyana.
Ba a jituwa tsakanin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP saboda bambance-bambancen ra'ayoyi da suke dasu.
Asali: Legit.ng