Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira

Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira

  • An yi kare jini, biri jini tsakanin mayakan ta’addancin ISWAP da na Boko Haram a jihar Borno inda aka halaka 8 daga cikin ‘yan Boko Haram
  • Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana tare da bidiyon yadda lamarin ya faru, an yi ne a yankin Krinowa dake Marte
  • Mayakan Boko Haram sun komai an yadda ‘yan ISWAP ke kokarin ganin bayansu tare da kwace sansanoninsu

Borno - Mayakan ta’addanci na ISWAP sun halaka mayaka takwas na kungiyar ta’addancin Boko Haram a wata arangama da suka yi a Borno.

ISWAP tsagi ne ba kungiyar ta’addancin Boko Haram kuma sun rabe ne sakamakon rikicin shugabanci.

Boko Haram
Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira. Hoto daga @Zagazolamakama
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, kungiyoyin ta’addancin biyu sun yi arangama ne a ranar Alhamis wurin Krinowa dake Marte.

An gano cewa ISWAP ce ta jagoranci wani harin kwantan bauna kan mayakan ta’addancin Boko Haram.

Gani Gado, Abou Adam da Abou Abubakar sune mambobin Boko Haram uku da suka sha da kyar da raunika.

An gano cewa ISWAP ta kwace tarin makamai daga mayakan Boko Haram din.

Zagazola Makama yace wata majiya tace Boko Haram sun aike tawagar mutum 12 daga Gaizuwa a Bama don su nemo makamai bayan artabun da luguden wutan da sojin Operation Hadi Kai suka musu.

Wannan nasarar ta bude kofar farmaki kan Boko Haram daga mayakan ISWy karkashin jagorancin Ba’ana Chigori.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, shugabannin Boko Haram sun yi taro inda suka aike tawagar mayaka 11 karkashin shugabancin Amir Bana Kaka domin neman goyon bayan Amir Jaichige a wuraren tsaunikan Mandara.

“Mayakan Boko Haram sun koka kan cewa mayakan ISWAP na iya kwace dukkan sansanoninsu kuma sun yi kira ga mayakan JAS da su taimaka musu kafin su rushe.”

- Majiyar tace.

Hamayya tsakanin kungiyoyin ta’addancin biyu yayi kamari ne lokacin da Abubakar Shekau ke shugabancin Boko Haram kuma aka kashe shi sakamakon arangama tsakanin ISWAP a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel