Jami'an Sojoji Sun Kwato Wata Jami’arsu Da ’Yan Bindiga Suka Sace, Suke Azabtarwa

Jami'an Sojoji Sun Kwato Wata Jami’arsu Da ’Yan Bindiga Suka Sace, Suke Azabtarwa

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kame wani da ya kitsa sace wata jami'ar soji tare da azabtar da ita a daji
  • An kuma ceto jami'ar da aka sace jim kadan bayan shiga aikin soja, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya
  • Ana yawan samun ayyukan ta'addanci a Kudu da Arewacin Najeriya a shekarun nan, musamman a 2022

Jihar Imo - Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar ceto wata jami’arta, Laftana P. P. Johnson da ‘yan bindiga suka sace a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda wasu ‘yan bindigan ke cin zarafin jami’ar bayan sace a garinsu, Ihube.

An ce ta yi tafiya zuwa garinsu ne daga wurin da take aiki don yin bikin kirsimeti a gida.

An ceto soja da aka sace, ake azabtarwa a Kudu
Jami'an Sojoji Sun Kwato Wata Jami’arsu Da ’Yan Bindiga Suka Sace, Suke Azabtarwa | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya ta soja:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PSC ta Dakatar da Jami’in da Ya Harbe Lauya Mai Ciki a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An sace ta ne a gidansu da ke Ihube. Ta yi tafiya ne don hutun bikin Kirsimeti.”

A wani bidiyon da aka yada, an ga lokacin da ‘yan bindigan ke cin zarafin jami’ar, inda suke barazanar kashe ta kasancewarta daya daga cikin sojojin Najeriya.

Haka kuma, sun yi gargadi ga matasan yankin Kudu masu Yamma kan shiga aikin tsaro da na gwamnatin Najeriya.

Hakazalika, an ga jami’ar a lokacin da take daure hannu da kafa tsirara tana zaune a kasa a cikin wani wuri mai alamun ciyawa.

An ceto jami'ar soji, an kama dan bindiga

Sai dai, daga baya rundunar sojin kasar ta bayyana cewa, an ceto wannan jami’ar soji tare da cafke wanda ya kitsa wannan aika-aika mara dadin ji, Politics Nigeria ta ruwaito.

Sakon rundunar ya bayyana cewa:

“Da misalin karfe 2:20 a ranar 29 ga watan Disamban 22, jami’an tsaro sun ceto da Lt P. P. Johnson da ‘yan bindiga suka sace tare da tafiya da ita cikin daji tsakanin Enugu da Ihube a karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo a ranar 26 ga watan Disamban 22.

Kara karanta wannan

Babban aiki: 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 21, sun ceto mutum 206 daga hannunsu

“Haka nan an kama wanda ya kitsa sace jami’ar kuma ana ci gaba da kokarin kame sauran masu hannu a ciki. Ana ci gaba da zuba ido kan lamarin ya zuwa yanzu."

'Yan ta'addan IPOB ne ke yawan aikata ta'addanci a Kudu maso Gabashin Najeriya.

A makon nan ne aka kama wasu 'yan ta'addan IPOB da ake zargin sun kashe tsohon jigon APC, Ahmad Gulak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel