Gwamna Soludo Ya Kara Tayin Afuwa Ga Yan Ta'adda da Suka Hana Zaman Lafiya

Gwamna Soludo Ya Kara Tayin Afuwa Ga Yan Ta'adda da Suka Hana Zaman Lafiya

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi kira ga 'yan bindiga da su aje makamansu za'a masu afuwa
  • Wannan ne karo na biyu da gwamnan ya yi tayin afuwa ga yan binidgan da suka hana mutane zaman lafiya a Anambra
  • A yan kwanakin nan dai hare-haren ta'addanci a Anambra da sauran jihohin shiyyar kudu maso gabas sun karu

Anambra - Gwamnan jihar Anambara, Charles Soludo, ya sake tayin afuwa ga 'yan bindigan da suka hana mutane zaman lafiya a jihar dake kudu maso gabashin Najeriya.

Gwamnan ya sanar da haka ne ranar Laraba yayin da yake jawabi ga manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambara.

Legit.n Hausa ta gano cewa gwamnan ya saka Bidiyon jawabin da ya yi a manhajar Youtube.

Gwamna Soludo na jihar Anambra.
Gwamna Soludo Ya Kara Tayin Afuwa Ga Yan Ta'adda da Suka Hana Zaman Lafiya Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Kamar dai sauran jihohin da ke shiyyar kudu maso gabas, Anambra na fama na yawaitar hare-haren ta'addancin 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Saboda yawan ganganci: Za a haramtawa 'yan sandan Najeriya shan giya gaba daya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A farkon shekarar nan dake gab da karewa ne wasu 'Yan bindiga sun kashe tare da cire kan wani ɗan majalisa. Haka kuma an yi garkuwa da tsoffin 'yan majalisa biyu daga baya aka kashe su.

Yan bindiga, waɗan da ake zargin wani bangare ne na kungiyar masu da'awar ballewa daga Najeriya, sun matsa kaimi wajen kai hari gine-ginen wasu kananan hukumomi.

Ku fito ku zama mutane nagari - Soludo

A jawabinsa, gwamna Soludo ya ce kofar gwamnatinsa a bude take na yi wa yan bindiga Afuwa domin su aje makamai kuma a basu horon yadda zasu zama mutane masu dogaro da kai.

Soludo ya ce:

"Muna son amfani da wannan dama mu sake kira ga wadanda ke cikin Daji, yan ta'addan da ke zaune a can da masu garkuwa su fito, muna muku tayin dama, zamu baku horo ku gina rayuwa mai amfani."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

Gwamnan yace akwai abun damuwa matuka yadda matasa suke lalata rayuwarsu wurin aikata muggan laifuka.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta basu, "sabuwar rayuwa" ga kowanensu da ya shirya aje makamai.

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ya yi tayin afuwa ga 'yan bindigan Anambra. Ya yi na farko a watan Yuli bayan ziyartar Nnamdi Kanu.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Hedkwatar 'Yan Sanda Ta Karamar Hukuma a Anambra

Rahoto daga wakilinmu na jihar Anambra ya nuna cewa wasu tsageru sun kai hari babban Ofishin yan sanda na ƙaramar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

Maharan sun bude wa yan sandan dake bakin aiki wuta kana daga bisani suka banka wa ginin wuta. Sun tafka mummunar ta'asa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262