Oyo: Wasu Tsageru Sun Je Har Gida Sun Halaka Mamban Jam'iyara PDP

Oyo: Wasu Tsageru Sun Je Har Gida Sun Halaka Mamban Jam'iyara PDP

  • Wasu tsageru sun je har gida sun halaka mamban jam'iyyar PDP, Mudashiru Baraka, a jihar Oyo ranar Laraba da safe
  • Sakataren watsa labarai na jihar Oyo, Akeem Olatunju, ya bukaci kwamishinan 'yan sanda ya kamo makasan su girbi abinda suka shuka
  • Har zuwa yanzun hukumar 'yan sanda ba ta ce komai ba a hukumance kan harin na Laraba 28 ga watan Disamba, 2022

Oyo - Rahoton da muke samu ya nuna cewa wasu miyagu sun yi wa mamba kuma jigon jam'iyyar PDP a jihar Oyo, Mudashiru Baraka, kisan gilla.

Ɗan siyasan ya rasa rayuwarsa ne a hannun tawagar 'yan daban da suke adawa da juna ranar Laraba 28 ga watan Disamba, 2022 da safe a garin Oyo.

Taswirar jihar Oyo.
Oyo: Wasu Tsageru Sun Je Har Gida Sun Halaka Mamban Jam'iyara PDP Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch Metro ta tattaro cewa Baraka, mamban PDP mai haɗa kan jama'a a matakin farko, an ce makasan sun daɓa masa makami ne har rai ya yi halinsa a gidan mahaifinsa da safe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da kisan

Jam'iyar PDP reshen jihar Oyo ta yi Allah wadai da lamarin inda ta koka cewa tana zargin harin ya samu goyon bayan wasu daidaikun mutane a tsagin 'yan adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jam'iyya mai mulkin jihar sauran mutanen da ke wurin sun gudu don tsira dauke da raunuka kala daban-daban a jikinsu.

Haka zalika PDP ta yi kira ga kwamishinan 'yan sanda, CP Adebowale Williams, ya gaggauta binciko makasan duk inda suka shiga domin doka ta hukunta su kan ɗanyen aikin da suka aikata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na Oyo, Akeem Olatunju, ya fitar ranar Laraba, ta nuna cewa an halaka mamacin aka barshi cikin jini a gidan iyayensa.

Sanarwan ta ƙara da cewa tuni dai aka kai rahoton abinda ya faru Ofishin 'yan sanda da ke Durbar a jihar Oyo, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saboda yawan ganganci: Za a haramtawa 'yan sandan Najeriya shan giya gaba daya

Har yanzu 'yan sanda basu ce komai ba

Duk wani kokari na jin ta bakin rundunar yan sanda ta bakin mai magana da yawunta, Adewale Osifeso, bai kai ga nasara ba sakamakon lambar wayarsa ba ta shiga.

A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Oyo Ya Rasu Yana Da Shekaru 62

Rahoto ya nuna cewa jigon siyasar ya riga mu gidan gaskiya ne a Asibitin jami'ar jiha da ke Ibadan babban birnin Oyo ranar Laraba 21 ga watan Disamba, 2022.

Marigayi Olayiwola, ya rike kujerar Sakataren jam'iyyar PDP ne a zamanin mulkin marigayi tsohon gwamnan Oyo, Adebayo Alao-Akala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel