Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Yan Sanda Suka Kama Sun Sheka Barzahu A Hanyar Zuwa Asibiti

Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Yan Sanda Suka Kama Sun Sheka Barzahu A Hanyar Zuwa Asibiti

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bakunci lahira a yayin da yan sanda ke hanyar garzayawa da su asibiti
  • Bright Edafe, mai magana da yawun yan sandan jihar Delta ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin wata tawagar masu garkuwa
  • Edafe ya ce sun kai yan sanda gidansu inda aka gano bindigu da adduna amma a hanyar mayar da su caji ofis sai suka yi yunkurin tserewa kuma yan sanda suka raunta su

Jihar Delta - Rundunar yan sanda ta jihar Delta ta tabbatar da mutuwar wasu masu garkuwa da mutane biyu da ke adabar Warri da kewaye.

Leadership ta rahoto cewa an kama su ne a daren ranar 24 a watan Disamba yayin da yan sandan 'B' Division ke sintiri a Warri a kan hanyar shataletalen Okumagba Estate a karamar hukumar Warri ta Kudu.

Kara karanta wannan

Daga Shiga Motar Haya a Titi, An Halaka Matasa 3 Tare da Cire Sassan Jikinsu

Taswirar Delta
Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Yan Sanda Suka Kama Sun Sheka Barzahu A Hanyar Zuwa Asibiti. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tsare wadanda ake zargin kuma yayin amsa tambayoyi sun amsa cewa su mambobin wata gungun masu garkuwa ne na mutum biyar da suke adabar mutanen Warri da kewaye.

Kakakin yan sandan jihar Delta, Bright Edafe ya ce masu garkuwar sun amsa cewa su mambobin gungun masu garkuwa na mutum biyar ne.

Masu garkuwan sun yi yunkurin tserewa daga hannun yan sanda - Edafe

Ya ce:

"Bisa bayanin da suka yi, wadanda ake zargin sun jagoranci yan sanda zuwa maboyarsu a wani gida da ke Upper Erejuwa Street, inda aka gano AK49 mai lamba 11876, da double barrel kirar gida da adduna biyu.
"A hanyar dawo da su caji ofis, wadanda ake zargin sun daka tsalle daga motar yan sandan da nufin su tsere, amma jami'an suka bi sahunsu."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Kebbi, Sun Kashe Mutum Biyu Tare Da Garkuwa Da Wasu 10

Edafe ya cigaba da cewa a yayin kokarin hana su gudu, yan sandan mun musu rauni suka sake kama su, sannan sun mutu yayin da ake hanyar kai su asibiti.

Mai magana da yawun yan sandan ya kara da cewa yan sanda na kokarin kamo sauran mambobin tawagar.

An kama masu garkuwa da mutane da yan bindiga 16 a Zamfara

Yan sandan jihar Zamfara ta kama wasu mutum 16 da ake zargin yan fashin daji ne da masu garkuwa da mutane kan aikata ta'addanci.

Mai magana da yawun yan sanda, Mohammed Shehu ya sanar da hakan yayin holen wadanda ake zargin ga manema labarai a madadin kwamishinan yan sanda Kolo Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164