Bayan an Tabbatar Jariri Ya Mutu a Cikin Mahaifa, Mata Ta Haife Shi Lafiya Kalau, Da Ransa

Bayan an Tabbatar Jariri Ya Mutu a Cikin Mahaifa, Mata Ta Haife Shi Lafiya Kalau, Da Ransa

  • Wata mata ta haifi jaririnta mai ban mamaki bayan da aka sanar da ita cewa, jaririn ya riga da ya mutu a mahaifanta
  • A farko an garzaya da matar zuwa asibiti lokacin da ta fara nakuda inda daga bisani aka bata mummunan labarin mutuwar jaririnta
  • Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun shiga mamaki, sun bayyana martaninsu tare da yi mata murna

Wata uwa mai kananan shekraru, Hannah Cole ta samu albarkar rayuwa daidai lokacin kirsimeti yayin da ta haifi jaririnta ta wata hanya mai ban mamaki.

A cewar wani rahoton Mail Online, lokacin da Hannah Cole ta fara nakuda, likitoci sun fada mata cewa, ai dama tuni jaririn ya mutu a cikin mahaifarta saboda basu ji alamar motsi ko bugun zuciyarsa ba.

A cewar rahoton, Hannah ta nemi likitocin da su sake yi mata hoton ciki, saboda tana ji a ranta jaririnta na raye.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Magana Game Da Jarumar Da Take Fitowa A Shirin Nan Mai Dogon Zango Na Amaryar Tik-Tok

Uwa ta haifi jariri duk da likitoci sun tabbatar ya mutu a mahaifa
Bayan an Tabbatar Jariri Ya Mutu a Cikin Mahaifa, Mata Ta Haife Shi Lafiya Kalau, Da Ransa | Hoto: Credit:@dailymail
Asali: Instagram

Da kanta tace ta gode Allah da aka ciro mata jaririnta a raye, ta yi imanin cewa, wannan kyauta ce daga Allah a bikin kirsimeti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin jama’a a yanar gizo

Mutane da yawa sun nuna sha’awa da wannan labari na Hannah bayan da ta tace ta haifi jaririnta lafiya, domin sun shiga mamakin yadda lamarin ya juya, suka taya ta murnar samun rabo.

Labarin da majiya ta yada a kafar Intagram ya dauki hankali, mutane sun martani ga kuma dangwalen nuna sha’awa da suke ta yi.

Kalli bidiyon:

Ga kadan daga ciki:

@nicemazatlan:

“Kimiyya ta ce a’a, ubangiji kuwa yace: NI NE!.”

@itstdrew:

"Kira shi zai sauya duniya.”

@linda_whitmire7:

"Allah ya miki albarka da ke da jaririn kullum shi ke kiran yana son ki same shi.”

@huffle_puff07714:

"Mu’jizozi na faruwa a ranar kirisimeti.”

@_olanla:

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

"Kullum ubangiji kan sanya kimiyya ta bayyana a matsayin shiririta.”

@kylecorwith:

"Ina tunanin wancan likitan na zubar da ciki ne amma kuma mahaifiyar mai son rayuwa ce.”

Dan Karamin Yaro Ya Shammaci Iyayensa, Don Ya Kurbe Barasar Babansa a Gida, Ya Shiga Hannu

A wani labarin kuwa, wani yaro ya kurbi barasar da mahaifnsa ya ajiye a cikin gida, lamarin da ya fusata mahaifin nasa.

Mahaifiyar yaron ta ba da hakuri yayin da take kyalkyalewa da dariya, mahaifin ya gargadi dan nasa.

Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani mai daukar hankali tare da daura laifin kan mahaifin da yake shan barasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel