Dan Karamin Yaro Ya Shammaci Iyayensa, Don Ya Kurbe Barasar Babansa a Gida, Ya Shiga Hannu

Dan Karamin Yaro Ya Shammaci Iyayensa, Don Ya Kurbe Barasar Babansa a Gida, Ya Shiga Hannu

  • Wani uba ya kama dansa hannu dumu-dumu yana kurbar barasarsa da ya aje a gida, ya tuhume shi a tsakiyar gida
  • Yayin da ya rutsa yaron, uban ya kura masa ido yana jiran ya yi bayanin me yasa ya sha barasar kuma yana karami dashi
  • Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun ce watakila yaron yana son sanin dandanon abin shan da mahaifinsa ke sha ne

A wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta, wani uba ya rutsa dansa a daidai lokacin da yake shanye masa barasa, lamarin da ya jawo cece-kuce a shafin sada zumunta.

A bidiyon, an ga lokacin da yaron ke tsaye a gaban mahaifin nasa, ana tuhumar me yasa ya tsoma kansa ga taba abin da bai shafe shi ba.

Mahaifiyar yaron, jessicaseth_ da tace yaron dariya ya ba ta, ta ci gaba da kyalkyalewa da dariya a cikin bidiyon.

Kara karanta wannan

Ta gudu ta barni: Dan acaba mai yawo da jariri a cikin riga ya fadi tarihinsa mai ban tausayi

Jeremya ya taro rikici, ya kurbi barasar mahaifinsa
Dan Karamin Yaro Ya Shammaci Iyayensa, Don Ya Kurbe Barasar Babansa a Gida, Ya Shiga Hannu | Hoto: TikTok/@jessicaseth
Asali: UGC

Mahaifiyarsa ta ba da hakuri a madadinsa

Ta kuma yi ta tambayar me yasa ya kurbi barasar, amma yaron ya yi shuru ya gaza cewa komai a ciin bidiyon.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan da matar ta nemi hakuri, mijin ya kori yaron tare da umartarsa ya nemi wurin zama ya zauna a dakin da suke tare a lokacin.

Kalli bidiyon:

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutum 200 ne suka yi martani, mutum 10,000 kuma sun yi dangwalen nuna sha’awarsu ga bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Ga kadan daga martanin jama’ar soshiyal midiya da muka tattaro muku:

Okikiola Safidiya:

“Kalli yadda uban yake kallonsa.”

Konboye Ziegbe:

"Mutum ya ga babansa na shan wani abu..babansa ke sha, babu abin da ya sami babansa..amma kuna tambayarsa me yasa ya sha nasa..amma dai wasa kuke ko?”

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Greg Bradford:

"An yi sa’a bai kyalkyale da dariya a gabansa ba..Don haka ya sake gwadawa.. Mama don Allah ki gargade shi kema saboda ya san ba ruwa bane ba kuma jus bane.”

user5853947868021:

"Jeremy ya yi alama da abubuwan ban mamaki yau kenan.”

Ibili Doris:

"Abin da da na zai iya yi kenan, wannan yamutsa fuska zai sa na yarda dashi.”

Wani uba kuma gargadi ya yiwa diyarsa da za ta tafi makaranta, yace kada ta dawo gidansa sai ta kammala digiri da '1st class'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel