Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini a Fitacciyar Jihar Arewa
- Mahara da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace limanin cocin katolika na Jihar Benue, Rabaran Fada Mark Ojotu
- Sanarwar da cocin katolika na Benue ta fitar ya an sace malamin addinin ne a kan hanyar Okpoga zuwa Ojapo a ranar Alhamis misalin karfe 5 na yamma
- Rundunar yan sandan jihar Benue ta bakin kakakin ta Catherine Anene, ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce suna kokarin ceto malamin addinin
Jihar Benue - Yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane sun sace limanin cocin katolika na Jihar Benue, Rabaran Fada Mark Ojotu.
An ce Ojotu shi ne Faston Asibitin St. Mary’s, Okpoga, a karamar Hukumar Okpokwu ta Jihar Benue a karkashin Diocese na Otukpo, rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sace shi ne a kan hanyar Okpoga zuwa Ojapo a ranar Alhamis misalin karfe 5 na yamma, rahoton The Punch.
Cocin ta tabbatar da sace shi cikin wasika mai dauke da sa hannun Rabaran Fada Joseph Itodo, inda ya bukaci sauran fastocin su cigaba da addu'a kuma kada su cire tsammani.
Wani sashi na wasikar ta ce:
"Mun rubuta wannan ne don sanar da ku sace daya cikin faston mu, Rabaran Fada Mark Ojotu.
"Shi ne malamin Asibitin St. Mary, Okpoga. Abin bakin cikin ya faru yau 22 ga watan Disambar 2022 misalin karfe 5 na yamma kan hanyar Okpoga zuwa Ojapo, karamar hukumar Okpokwu, jihar Benue.
"Most Rabaran Michael Ekwoyi Apochi, yana kira ga dukkan kiristoci a cocin katolika na Otukpo da sauran wuri su yi addu'ar sakinsa cikin gaggawa a yayin da muke kokarin ceto shi."
Martanin yan sandan Benue kan sace malamin addinin
Mai magana da yawun yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta kara da cewa yan sanda na bin sahun masu garkuwan.
Anene, cikin sakon kar ta kwana da ta aike wa wakilin majiyar Legit.ng Hausa ta ce:
"Lamarin ya faru kuma rundunar tana bin sahun malamin addinin da bata-garin da suke da hannu."
Yan bindiga sun sace fasto a cocinsa a jihar Ondo
A wani rahoton kun ji cewa wasu mahara da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon daga da Ogedengbe, faston cocin Deeper Life da ke garin Irese a karamar hukumar Akure South a jihar Ondo.
The Nation ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Mayun 2021 a harabar cocinsa.
Maharan sun taho cocin ne cikin wata mota kirar Toyota Corolla a cewar wani shaidan gani da ido kuma mamba a cocin.
Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku
Asali: Legit.ng