‘Yan Kasuwa Na Lissafin Sayen Mai a N148, Tinubu Ya Dage Sai An Cire Tallafin Fetur
- Bola Tinubu ya hakikance a kan cewa janye tallafin man fetur ne zai taimaki tattalin arzikin Najeriya
- ‘Dan takaran na APC yana ganin tsarin yana amfanar kasashen da ke makwabtaka da kasar nan ne kurum
- Idan gwamnati ta cire hannunta, farashin kowane litan fetur a gidan mai zai iya zarce N400 a shekarar badi
Abuja - Kamfanin man Najeriya watau NNPCL yana shirin shiga yarjejeniya da ‘yan kasuwa domin su rika karbar sarin duk litar man fetur a kan N148.
Wani shugaba a kungiyar IPMAN masu dakon man fetur a Najeriya, Mike Osatuyi ya shaidawa jaridar Punch cewa su na tattaunawa da kamfanin NNPCL.
‘Yan kungiyar IPMAN sun zauna da Darektan saide-saide na NNPCL, Hubb Stockman wanda ya yi masu alkawarin za a rika saida masu fetur kai-tsaye.
Idan aka sa hannu a yarjejeniyar nan, za a tilasta saidawa ‘yan kungiyar litar man a kan N148, ba tare da sun je tashoshi ba, su kuma su kai gidajen mai.
Zuwa Junairu za a ji alheri - Osatuyi
“Su (NNPCL) sun sa IPMAN a karkashin (Stockman) kai-tsaye, kuma mutumin kirki. A zaman da muka yi tayi da shi, za a ji alheri nan da watan Junairu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Za mu samu kaya kai-tsaye daga NNPCL, kuma ba za mu sha wahalar zuwa tasha ba. Bature ne shi, kun san turawa ba su siyasa. A haka farashi zai sauka.
Amma abin da muke so shi ne a daure a haka, ka da ya zama a fara sai a daina.
- Mike Osatuyi
Wani shugaban IPMAN, Akin Akinrinade ya ce a kan fiye da N200 ake saida masu mai a tashoshi. Hakan ya sa dole lita ya kai N250 a gidajen mai.
Ra'ayin Tinubu a kan tallafin man fetur
Ana haka ne sai rahoto ya zo cewa Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC yana cewa dole a janye tallafin man fetur.
This Day tace da yake magana a ranar Alhamis, Bola Tinubu ya ce duk yadda za ayi bore domin a bar tallafin, wajibi ne gwamnati ta yi fatali da tsarin.
‘Dan takaran na APC ya yi alkawarin kawo karshen matsalar biyan tallafin da zarar ya zama shugaban kasa, ya ce zai rufe ido ya yi abin da ya kamata.
Hadimin ‘dan takaran, Tunde Rahman ya rahoto shi yana cewa tsarin yana jawo Najeriya ta na saida man fetur da araha ne ga Kamaru, Nijar da Benin.
Harajin sadarwa a Najeriya
A yau muka samu rahoto ‘Yan majalisar tarayya za su tattauna a kan tsarin karbar harajin sadarwa a kowane wata daga kamfanonin da suke aiki a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta sake dauko wannan batu wanda a dalilin Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami aka yi watsi da shi a kwanaki.
Asali: Legit.ng