Gwamnatin Buhari na Kokarin Dawo da Harajin da Isa Pantami Ya Hana a Kakaba a 2022

Gwamnatin Buhari na Kokarin Dawo da Harajin da Isa Pantami Ya Hana a Kakaba a 2022

  • Gwamnatin tarayya ta na la’akari da tsarin karbar haraji daga duk wani kamfanin sadarwa a Najeriya
  • Maganar ta je gaban ‘yan majalisa domin a tattauna a kai, tsarin zai fara aiki a 2023 idan ta tabbata
  • A lokacin da gwamnati tayi niyyar lafta harajin, Isa Ali Pantami ne ya bada shawarar ayi watsi da shi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta na duba yiwuwar lafta haraji a kan harkokin sadarwa bayan an dakatar da maganar, hakan zai jawo yin waya ya kara tsada.

Wani rahoto da muka samu daga Punch a ranar Juma’a ya nuna gwamnatin tarayya ta sake bijiro da wannan batu domin a aiwatar da shi a shekarar 2023.

Wannan bayani na cikin wata takarda da aka gani da za a gayyaci mutane domin tattauna kudirin tattalin arzikin 2022 a zauren majalisar wakilan tarayya.

Kara karanta wannan

Matsalolin da Aka Samu a Kundin 2023 Ya Hana a Amince da Kasafin Kudin Najeriya

Kwamitin harkar tattalin arziki na majalisar tarayyar kasar ya fitar da wannan takarda.

Ta koma, ta leko...

An fahimci harajin sadarwar da aka dakatar a shekarar nan, yana iya komawa gaban ‘yan majalisar wakilan Najeriya a kokarin da ake yi na samun kudin shiga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamitin harkar kudin ya ce zai zauna da al’umma domin jin ra’ayinsu a kan kudirin tattalin arziki na shekarar 2022, kuma za a tabo maganar harajin.

Gwamnatin Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: Muhammad M. Nami
Asali: UGC

Daga cikin abin da takardar kudirin take cewa shi ne Najeriya za ta rika karbar haraji daga kamfanonin sadarwa a karkashin sashe na 13 na wannan doka.

Shugaban kasa ne yake da ikon yanke kason harajin da za a karba a wajen kamfanonin.

Rahoton ya ce kudirin ya nuna babban dalilin hakan shi ne ya taimaka wajen kara kudin shiga da harajin da gwamnatin tarayya za ta rika samu a shekara.

Kara karanta wannan

Sabuwar kitimurmura: Ba mu san adadin sabbin Naira da aka buga ba, inji CBN

Nawa za a rika karba?

A takardar, ba ayi bayanin adadin harajin da za a rika yankawa kamfanonin sadarwar da ke kasar ba. A karshe dai za a tashi da biliyoyin kudi a asusu.

A watan Yulin 2022 da aka bijiro da tsarin, an yi niyyar karbar harajin 5% kamar yadda yake a kudirin tattalin arziki tun 2010, amma ba a iya aiwatar da shi ba.

Kafin ranar 21 ga kowane wata ya kamata kamfanoni su biya harajin. Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ne ya roki a hakura saboda farashin waya zai tashi.

Bashir Machina v Ahmad Lawan

Idan aka shiga siyasa, za a ji labari kwamitin yakin neman zaben Bashir Machina a APC, ya ce Dr. Ahmad Lawan yana cin amanar Bola Tinubu a takarar 2023.

Amma kakakin kwamitin takarar Tinubu, Festus Keyamo ya karyata zargin, ya ce Lawan ba zai taba yin watsi da ‘dan takaran APC saboda Atiku Abubakar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel