Matsalolin da Aka Samu a Kundin 2023 Ya Hana a Amince da Kasafin Kudin Najeriya

Matsalolin da Aka Samu a Kundin 2023 Ya Hana a Amince da Kasafin Kudin Najeriya

  • Shugaban Majalisar dattawa ya ce ba za ta yiwu a kammala aiki a kan kundin kasafin kudin 2023 ba
  • Dr. Ahmad Lawan ya ce an samu wasu matsaloli a tattare da kasafin kudin da aka gabatar a watan Oktoba
  • Lawan bai yi karin bayani a kan cikas din da aka samu ba, amma ya nuna kwamitoci su na aiki a kai

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta dakatar da maganar amincewa da kasafin kudin 2023 zuwa mako mai zuwa bayan an gamu da wasu ‘yan matsaloli.

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Lawan ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis. Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

Dr. Ahmad Ibrahim Lawan yake cewa ‘yan majalisar tarayya ba za su iya yin na’am da kundin kasafin kudin na badi domin ‘ya zo da wasu ‘yan matsaloli’.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya Ya Jero Wadanda Za Su Fi Shan Wahalar Canjin Kudi da Aka Yi

Lawan ya ce kwamitin kasafin kudi na majalisa ya gano wadannan matsaloli a kundin. Shugaban majalisar ya yi wannan bayani a shafin Facebook.

Ahmad Lawan
Shugaban majalisar Dattawa Hoto: @DrAhmadLawan1
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Sanata Ahmad Lawan

Kundin kasafin kudi ya zo majalisar tarayya da wasu matsaloli da kwamitocin kasafinmu na majalisar dattawa da wakilan tarayya suka zauna domin ganin abin da za a yi da kuma abin da za a gabatar.
Matsalolin sun fito karara kuma an gaza magance su, dole kwamitocin suka fara aikin daga farko domin gyara kasafin kudin. Aikin ya kai an zauna da bangaren zartarwa domin daga wurinsu matsalar ta fito.
Sai a jiya ne kwamitocin suka kammala aikinsu.

- Ahmad Lawan

Rahoton ya ce shugaban majalisar bai iya bayanin wadannan matsaloli da aka ci karo da su ba.

Abin da Lawan ya shaidawa Duniya shi ne kwamitocin ba su iya kammala aiki domin gabatar da rahotonsu ba, kuma ba za a iya karasa aikin gobe ko jibi.

Kara karanta wannan

Ana Kukan Bashi Ya Yi Katutu, Buhari Yana Kokarin Sake Karbo Aron N0.8tr

Haka zalika Shugaban Sanatocin ya ce ba za ta yiwu kwamitocin majalisun su karkare gyara matsalolin a farkon makon gobe ba saboda hutun da za ayi.

Ba za ta yiwu a amince da kasafin kudin sai zuwa ranar Laraba 28 ga watan Disamba.

Ina tare da Bola Tinubu/Kashim Shettima - Buhari

Dazu an ji labari Muhammadu Buhari ya ce zai goyi bayan Bola Tinubu/Kashim Shettima sai inda karfinsa ya kare domin ‘dan takaran ya zama magajinsa.

Duk da alkawarin da ya yi wa‘dan takaran shugaban kasar, Buhari ya ce mulkin Najeriya zai fi cin lokacinsa a kan yawon tallata Tinubu a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel