Ba Mu San Adadin Sabbin Naira da Aka Buga Ba, Inji Babban Bankin Najeriya

Ba Mu San Adadin Sabbin Naira da Aka Buga Ba, Inji Babban Bankin Najeriya

  • Wakiliyar da ta wakilici Babban Bankin Najeriya (CBN) ta ce bata san adadin kudaden da aka buga suke yawo a Najeriya ba
  • Majalisar wakilai ta kasa ta nemi ganin gwamnan CBN ko mataimakiyarsa don amsa wasu tambayoyi da ke da alaka da sabbin Naira
  • Babban bankin na CBN ya sauya fasalin Naira a shekarar nan, ana ta cece-kuce kan gwamutsuwar sabbin kudin da na bogi

FCT, Abuja - Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad ta bayyana cewa, bata san adadin kudin da aka buga kuma suka fara yawo a Najeriya ba.

Ta bayyana hakan ne yayin da ta wakilci mai girma Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a majalisar kasa don yiwa 'yan majalisar wakilai bayanin shirye-shirye da sabbin ka'idojin kudi na bankin kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Majalisar ta yanke a ranar Laraba 21 ga watan Disamba cewa, dole mataimakiyar gwamnan CBN ta bayyana a gabanta a ranar Alhamis domin yin karin haske game da dokokin kudi a kasar.

Aisha Ahmed ta ce bata san adadin kudin da CBN ya buga ba
Ba Mu San Adadin Sabbin Naira da Aka Buga Ba, Inji Babban Bankin Najeriya | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Majalisar ta ba gwamnan CBN uzurin bai da lafiya don haka ba zai samu damar halartar wannan zama ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ake ganin karancin sabbin Naira a Najeriya?

Da yake tambayar titisye ga Aisha Ahmed, dan majalisa Sada Soli ya kawo batun karancin sabbin Naira a Najeriya kwanaki kadan bayan fara kashe kudin a kasar, don haka ya nemi ta yi bayani.

Da take martani, ta ce sam bata san adadin kudaden da babban bankin ya buga ba, don haka ba ta da amsar dalilin karancin kudin.

Ana ci gaba da kai ruwa rana a Najeriya kan gane sabbin Naira na gaske da na bogi tun bayan fara kashe sabbin kudin da CBN ya buga.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Wakiliyar Emefiele Tana Jawabi Gaban Majalisar Wakilan Najeriya

Sai dai, ta ba da tabbacin cewa, a yanzu haka an ba da odar buga kudin da ya kai N500m don sake rabawa bankuna a Najeriya, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Ta yaya za mu yarda da hukumomin kasar nan?

Wani masanin tattalin arziki kuma malamin jami'a, Muhammad Shamsudden Sani ya zanta da wakilin Legit.ng Hausa, inda ya bayyana kadan daga ra'ayinsa game da batun rashin sanin adadin kudaden da aka buga.

A cewarsa:

"Akalla dai ana zaman tattaunawa a CBN, kuma tsakani da Allah ace mataimakiyar gwamna bata san adadin kudaden da aka buga ba, wannan magana akwai rashin sanin aiki a ciki.
"Ta yaya za mu yarda kuma mu aminta da ma'aikatan kasar nan? An daura ku ku yi aiki, amma baku san aikin da kuke ba.
"Ku 'yan jarida sun fi ma'aikatan gwamnati sanin halin da kasar nan ke ciki."

An kara adadin kudin da 'yan Najeriya za su iya cirewa a banki

Kara karanta wannan

Bankin Duniya Ya Jero Wadanda Za Su Fi Shan Wahalar Canjin Kudi da Aka Yi

A wani labarin kuma, kunji yadda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yiwa sabbin dokokin kayyade cire kudi a banki kwaskwarima duba da bukatun 'yan kasar.

CBN ya ce, a yanzu mutum zai iya cire kudin da suka kai N500,000 sabanin N100,000 a farkon dokar duk mako.

Hakazalika, asusun kamfani zai iya cire kudin da ya kai N5,000,000; sabanin N500,000 da a farko CBN yace ya amince a cire duk mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel