Yar Sani Abacha tayi bikin zagayowar ranar haihuwarta cikin girma (hotuna)
Legit.ng ta ci karo da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar Gumsu, daya daga cikin yaran tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Sani Abacha.
Gumsu Abacha-Fadil, ta kara shekaru a duniya a ranar 23 ga watan Satumba sannan ta yanke shawarar raya wannan rana tare day an uwa da abokan arziki.
Matashiyar wacce ta kasance daya daga cikin shahararrun yayan tsohon shugaban kasar ta fito shar da ita a wannan rana mai matukar muhimmanci gare ta.
Mahaifiyarta, tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Maryam, ta kasance a wajen taron don taya yar ta murna.
KU KARANTA KUMA: Amurka ta sanya sabon tarnakin shiga kasar a kan kasashe 8
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma
Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng