Kamfanin BUA Ya Ba Da Tallafin Kujeru Da Tebura Ga Makarantu a Jihar Sokoto

Kamfanin BUA Ya Ba Da Tallafin Kujeru Da Tebura Ga Makarantu a Jihar Sokoto

  • Kamfanin simitin BUA ta yiwa makarantu sha tara ta arziki domin karfafa harkar ilimi a jihar Sokoto
  • A kokarin samawa dalibai yanayi mai kyau don jin dadin karatu, kamfanin BUA ya ba da gudunmawar kujeru da tebura 1,000 ga makarantu
  • An yi kiyasin kudin kujerun ya kai kimanin naira miliyan 32 kuma makarantun gwamnati da na Islamiyya da dama za su ci gajiyar shirin

Sokoto - Kamfanin simintin BUA ya fara rabon kujeru da tebura mai cin mutum uku guda 1,000 wanda farashinsu ya kai naira miliyan 32 ga makarantu a fadin jihar Sokoto.

Wannan tallafin na daga cikin jajircewar kamfanin na tallafa garuruwan da suka karbi bakuncinsa, jaridar Leadership ta rahoto.

Shugaban kamfanin BUA
Kamfanin BUA Ya Ba Da Tallafin Kujeru Da Tebura Ga Makarantu a Jihar Sokoto hOTO: Nairametric
Asali: UGC

Makarantu 13 za su amfana da wannan tagomashi

A jawabinsa yayin rabon kayayyakin ga daya daga cikin makarantun, Alhaji Sada Sulaiman, jigon kanfanin simintin BUA ya bayyana cewa makarantu 13 ne za su amfana daga wannan tallafi a jihar.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Sulaiman:

"Wannan zai amfani wasu makarantun gwamnati da na Islamiyya ciki harda Assasul Ilam Arkilla, Ma'ahadu Abdullahi Nakasari da Madrasatul Anas Bin Malik Bado.
"Hakazalika makarantar Sakandare na Sultan Atiku, makarantar Firamare na Gidan Salanke, makarantar firamare Wamakko, Marafa Danbaba Nizamiyya, Aishatu Ummul Muminina Arkilla, makarantar firamare na Asare, makarantar firamarr na Wajeke, makarantar firamare na Gwuiwa da makarantar BUA Cement za su amfana."

A nashi bangaren, Alhaji Abdulganiyu Yussuf, Daraktan harkokin siye da siyarwa na kamfanin simintin BUA ya bayyana cewa wannan shiri don nuna godiya ne ga manufar gwamnatin jihar Sokoto na ayyana dokar ta baci kan ilimi.

Ya ce:

"Tabbass muna cikin wannan hadaka na tabbatar da nasarar manufofi da tsare-tsaren gwamnati. Za mu raba akalla kujeru da tebura mai cin mutum uku guda 1,000, wanda farashinsu ya kai naira miliyan 32 don samar da yanayin karatu mai kyau ga dalibanmu.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Kunno a PDP Yayin da Atiku Abubakar Da Tawagarsa Zasu Shiga Katsina Yau

"Saboda haka, ina umurtan makarantun da suka amfana da su yi amfani da wannan karamcin yadda ya kamata domin cimma nasarar abun."

Da yake martani a madadin wadand suka amfana, Alhaji Abubakar Chika, sakataren karamar hukumar Wamakko ya nuna godiya ga kamfanin simintin BUA kan gudunmawar nasu yana mai cewa wannan zai wayar da kan sauran yan kasuwa a fadin jihar, rahoton The Sun.

Karamin yaro ya aika sako ga Peter Obi

A wani labarin, wani karamin yaro ya roki Peter Obi da kada ya baiwa yan Najeriya kunya idan har suka zabe shi a babban zaben shugaban kasa na 2023.

Yaron ya nuna karfin gwiwar cewa Obi zai iya magance matsalolin da suka dabaibaye Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel