Jami’in DSS Ya Harbi Matashi a Wajen Gangamin APC a Jihar Gombe
- Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi umurnin kama jami’in DSS da ya harbi wani matashi
- Auwal Hassan ya bi sahun daruruwan mazauna kauyen Bojude da suka yi tururuwa a wajen gangamin yakin neman zaben APC amma sai tsautsayi ya hau kansa
- Gwamnan na Gombe ya baiwa matashin da wasu hudu mukamai a matsayin hadimansa na musamman
Gombe - Daily Trust ta rahoto cewa jami'in DSS ya harbi wani matashi mai shekaru 30, Auwal Hassan, a wajen gangamin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba a garin Bojude da ke karamar hukumar Kwami ta jihar Gombe.
Wanda abun ya ritsa da shi ya bi sahun sauran mazauna kauyen wadanda suka yi tururuwa don tarbar tawagar yakin neman zaben Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Wani ganau ya shaida ma jaridar cewa harbin jami'in na DSS ya fita sannan ya samu Hassan a kafarsa yayin wani dan hatsaniya bayan ayarin motocin gwamnan sun isa wajen taron gangamin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa matashin ya fadi a kasa cikin zafin ciwo bayan an harbe shi, lamarin da ya tunzura sauran matasa suka fara ihun 'Ba ma yi' a wajen kamfen din.
Sai da sauran jami'an tsaro da ke ayarin gwamnan suka shiga lamarin kafin matasan suka yarda suka sauko.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi umurnin kama jami'in DSS da ya harbi matashi
Da yake jawabi ga taron jim kadan bayan afkuwar lamarin, Gwamna Yahaya ya yi umurnin gaggauta kama jami'in DSS din don bincike, rahoton The Guardian.
Ya kuma yi umurnin cewa a dauki wanda abun ya ritsa da shi zuwa asibiti don samun kulawar likita daga asusun gwamnatin jihar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewar ya nada wanda abun ya ritsa da shi tare da wasu matasa hudu daga garin Bojude a matsayin hadimansa na musamman.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Mu'azu Abubakar, ya nemi a bashi lokaci don samun cikakken bayani kan lamarin amma ba a ji sa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Ohanaeze ta karyata kashe yan arewa 100 a kudu maso gabas
A wani labari na daban, kungiyar Inyamurai ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin kashe yan arewa 100 a yankin kudu maso gabas a makon da ya gabata.
A cewar Ohanaeze Ndigbo wannan kanzon kuregen na iya tarwatsa kasar inda ta bukaci a kama wadanda suka kirkiri lamarin.
Asali: Legit.ng