Kwastan Motar Bas Ya Fusata, Ya Ki Karbar Sabon Kudi N1000 da Gwamnati Ta Kaddamar Kwanan Nan

Kwastan Motar Bas Ya Fusata, Ya Ki Karbar Sabon Kudi N1000 da Gwamnati Ta Kaddamar Kwanan Nan

  • Wata mata ta kusan shiga matsi a ranar Alhamis bayan da ta ba kwandastan mota sabuwar dubu da gwamnatin Buhari ta buga
  • An ga kwandastan a wani bidiyon da ya yadu a intanet, inda yace fasinjar ta sauka daga motar bas saboda ba shi sabon kudi
  • A ranar Alhamis ne sabon kudin da gwamnatin Najeriya ta sake ma fasali suka fara yawo a Najeriya

Wani bidiyon yadda kwandastan mota bas a jihar Legas ya ki karbar N1000 sabuwa bugu daga wata fasinja mace ya yadu a intanet.

A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba ne matar ta hau mota bas, sai ta zari N1000 sabuwar bugu da aka sauyawa fasali ta ba kwandasta, amma ya kekashe ya ki karba.

Kwastandan cikin tsoron kada a bashi jabun kudi ya ce sam ba zai karbi abin da bai da tabbas akai ba kuma bai saba ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: An Sake Samun Ibtila'in Fashewa a Babban Birnin Wata Jiha a Najeriya

Kwandasta ya ki karbar sabuwar N1000
Kwastan Motar Bas Ya Fusata, Ya Ki Karbar Sabon Kudi N1000 da Gwamnati Ta Kaddamar Kwanan Nan | Hoto: Instablog
Asali: Facebook

Daga matar kuma ta faraja dashi, tace bata da wani kudin da za ta iya bashi sai wannan gudan N1000.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin kwandasta ga N1000 sabuwar bugu

Alamu sun nuna dai wannan kwandasta tsoro yake watakila kudin ba na gaske bane, saboda yace ma matar kawai ta sauka tunda bata da wani kudin na daban.

Ta yi sa’a, mutanen da ke cikin motar suka lallabe shi kan ya karbi kudin tare da yi masa magiya da bayanin ai tuni sabbin kudi sun fara yawo.

Bidiyon wannan lamari ya jawo cece-kuce a shafin sada zumunta, mutane da yawa sun yi martani da ganin wannan lamari.

Martanin ‘yan Najeriya

@Iam_ogomzz:

“Ya kamata a kama wannan kwandastan, laifin ne a idon doka ya ki karbar kudin.”

@arikoko1:

“Ban ga laifinsa ba fa, wasu mutane da yawa basu san abin da ke faruwa a kasar nan ba.”

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

@michola94:

“Kudin da yanzu ya fito da safen nan! Ba ma za ta jira sai da yamma ba. Lallai kam. Mutane da samun dama.”

@Jhaysn1:

"A nan a PH, wata fasinja ta ki karban canjin tsohuwar 200 saboda ba sabuwa bace ba za ta karba ba...LoL...akwai dai matsaloli a kasar nan da yawa.”

Wata mata ta nuna ma duniya yadda ta yi ajiyar makudan kudade cikin shekara daya, ta ba kowa shawarin ya gwada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.