Sanusi, Soludo da Mutane 10 da Suka Rike CBN Kafin Godwin Emefiele a Tarihi

Sanusi, Soludo da Mutane 10 da Suka Rike CBN Kafin Godwin Emefiele a Tarihi

  • FCT, Abuja - Daga lokacin da aka kafa babban bankin Najeriya a 1958, an yi mutane 12 da suka jagoranci CBN a matsayin Gwamnonin bankin
  • Wani rahoto da aka buga a Infomedia ya nuna Gwamnan bankin CBN na farko a tarihi shi ne Roy Pentelow Fenton, wani mutumin Birtaniya
  • A lokacin Fenton, ‘yan majalisar wakilan tarayya suka zo da dokar da ta kafa CBN a Watan Maris 1958, bankin ya fara aiki a Yulin shekarar 1959

1. Roy Pentelow Fenton

Roy Fenton ya rike babban bankin kasar har zuwa 1963 a lokacin da Najeriya ta zama tarayya.

Gwamnonin CBN da aka yi bayan nan:

2. Aliyu Mai-Bornu

A Yulin 1963 Gwamnatin Alhaji Tafawa Balewa ta nada Alhaji Aliyu Mai-Bornu wanda ya karanta ilmin tattalin arziki a jami’ar Bristol a matsayin Gwamnan CBN.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Jihar Kaduna Ta Cika Ta Batse Jiya Don Taron Kamfen APC

Tsohon malamin makarantar ya bar ofis a Yunin 1967, bayan shekaru uku Mai Bornu ya rasu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Clement Nyong Isong

Dr. Clement Nyong Isong masanin tattalin arziki ne da ya yi karatu har zuwa Digirin PhD a Iowa da Massachusetts a Amurka, ya rike CBN tsakanin 1967 da 1975.

Bayan Clement Isong ya yi Gwamnan CBN, ya rike kujerar Gwamna a jiharsa, ya rasu a 2000.

4. Adamu Ciroma

Tsakanin 1975 zuwa 1977, Gwamnan babban bankin Najeriya shi ne Mallam Adamu Ciroma. Bayan barin kujerar a Yunin 1977, ya yi ta rike mukaman Minista.

Tsakanin 1999 da 2003, Ciroma ya sake zama Ministan tattalin arziki, a shekarar 2018 ya rasu.

5. Olatunde Olabode Vincent

Bayan ya sauka daga kujerar mataimakin shugaban babban bankin cigaban Afrika, a 1977 Olatunde Olabode Vincent ya zama Gwamnan CBN na biyar zuwa 1982.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Kus-Kus da Wani ‘Dan Takaran 2023, Ya bar Magoya-baya a Duhu

6. Abdulkadir Ahmed

A tarihi babu wanda ya dade a CBN irin Abdulkadir Ahmed, tun 1982 ya shiga ofis har karshen Satumban 1993. Kafin nan shi ya fara zama Kwamishinan kudi a Bauchi.

Godwin Emefiele
Gwamnonin bankin CBN Hoto: National Archive
Asali: UGC

7. Paul Agbai Ogwuma

A 1993, Janar Sani Abacha ya dauko Akanta kuma Darektan bankin Union Bank, Dr. Paul Agbai Ogwuma ya zama Gwamnan CBN, bai sauka ba sai a watan Mayun 1999.

8. Joseph Oladele Sanusi

Da Olusegun Obasanjo ya dawo mulki, sai ya dauko Joseph Oladele Sanusi, ya kawo shi CBN. Sanusi ya zama shugaban SEC na farko a 1978, kuma ya rike bankin UBA.

9. Chukwuma Charles Soludo

Charles Chukwuma Soludo Farfesan tattalin arziki ne wanda daga Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki ya zama Gwamnan CBN a 2004 zuwa 2009.

10. Sanusi Lamido Sanusi

A 2009 Ummaru ‘Yar’adua ya nada Darektan bankin First Bank, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya jagoranci CBN. A 2014, Shugaba Goodluck Jonathan ya daka

Kara karanta wannan

2023: Saura Kwana 70 Zabe, Shugaban INEC Ya Tona Danyen Aikin da ‘Yan Siyasa Suke Yi

11. Sarah Alade

Bayan dakatar da Sanusi Lamido Sanusi, mace ce ta zama Gwamnan rikon kwarya. Mrs Sarah Alade tayi ‘yan watanni a ofis, kafin a nada wanda zai gaje ta a 2014.

12. Godwin Emefiele

A yau Godwin Emefiele ne yake rike da CBN tun Yunin 2014. Kafin a dauko shi, shi ne babban Darekta a bankin Zenith Bank Plc. Yanzu yana kan wa’adinsa na biyu.

Za a kama Gwamnan CBN da wasu jami'ai

An ji labari kwamitin da ya yi binciken kudi a Majalisa yace za a kama gwamnan babban banki, shugaban kamfanin NNPC, da shugabannin NDDC da RMFAC.

Binciken ya jawo EFCC za ta binciki jami’o’in Jos, Gusau, Akure, Ilorin da Abeokuta, kuma za maka shugabannin bankin FMBN zuwa wajen hukumar binciken.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng