Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Jihar Ebonyi, Sun Harbe Mutum Daya

Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Jihar Ebonyi, Sun Harbe Mutum Daya

  • Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare da addabar al'ummar jihar Ebonyi tare da durkusar da harkokin kasuwanci
  • Wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun farmaki kasuwa Nwakpu da ke yankin Ikwo
  • Bayan sun kora yan kasuwa tare da tilasta masu rufe shagunan sai suka harbe wani dan achaba da kona masa babur dinsa

Ebonyi - Wasu tsagerun yan bindiga a ranar Laraba, 14 ga watan Disamba, sun farmaki yankin Nsufu-Alike, garin Ikwo da ke karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi.

Maharan sun kai hari kasuwar Nwakpu da ke yankin inda suka harbi wani dan acaba a kai sannan suka cinnawa abar hawanda wuta.

Yan bindiga
Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Jihar Ebonyi, Sun Harbe Mutum Daya Hoto: Punch
Asali: UGC

Abun da ya faru

Wata majiya a garin wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigar sun farmaki kasuwar ne a lokacin da yan kasuwa suka bude harkokin kasuwancinsu a safiyar Laraba.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Buhari Ya Yi Magana Kan Gaskiyar Bacewar Naira Tiriliyan 89 a Bankuna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta rahoto cewa kasuwar ta Nwakpu tana kallon mahaifar mataimakin gwamnan jihar Ebonyi, Eric Kelechi.

Majiyar ta ce:

"Yan bindigar sun shigo kasuwar sannan suka umurci yan kasuwa da masu shago da su bar kasuwar. Sun kuma fada masu cewa su bi umurnin zaman gida.
"Bayan sun kora yan kasuwa da masu shagon, sai yan bindigar suka cinnawa wata babur wuta. mai babur din ya yi kokarin kashe wutar, sai yan bindigar suka harbe shi a kai da kafa."

Harkokin kasuwanci sun tsaya cak

Hakazalika, an tsayar da harkokin kasuwanci a Abakaliki, babban birnin jihar yayin da aka rufe gidajen mai, bankuna da wuraren taro don bin dokar zama a gida, rahoton Daily Post.

Da yake tabbatar da lamarin, kwamandan kungiyar Ebubeagu, Mista Friday Nnanna ya ce maharan ba mambobin kungiyar IPOB bane illa yan daba wadanda suka farmaki kasuwa don yiwa yan kasuwa fashin kayansu.

Kara karanta wannan

Dan Ba Kara Zaben APC A 2023: Mun Zabi Buhari Wahala Ta Kusan Kashe Mu, iInji 'Yan Arewa

Ya kuma bayyana cewa suna nan suna aiki domin gano wadanda suka aikata ta'asar.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, kwamishinan yan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba, ya ce yana kan hanyar tafiya kuma ba zai iya amsa tambaya ba.

Na yi abun da zan iya a matsayin shugaban kasa, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya kasa ce mai girma da tarin matsaloli amma ya yi iya bakin kokarinsa a matsayin shugaban kasa.

Buhari ya ce gwamnatinsa na kokarin inganta rayuwar matasa domin dai sune shugabanni a gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng