Bidiyon Shawarin Wata Mata Na Yadda Mutane Zasu Iya Yin Asusun N1.2m a 2023 Ta Amfani da Ambulaf 100

Bidiyon Shawarin Wata Mata Na Yadda Mutane Zasu Iya Yin Asusun N1.2m a 2023 Ta Amfani da Ambulaf 100

  • Wata mata a kafar sada zumunta ta yanke shawarin muna ma duniya yadda ta yi asusun R50k (N1,290.634) a cikin ambulam guda 100
  • Matar a TikTok mai suna @nomazdiaries ta yi bayani a bidiyo, inda ta nuna yadda ta tsara kuma ta yi nasarar tara kudade masu yawa
  • Mutane da yawa a kafar sun yi mamaki, sun bayyana martani da kuma yaba irin wannan dabi’a da take bi na tara kudade

Ajiya an ce maganin wata rana, amma wani lokacin yana da matukar wahala mutum ya iya ajiyan kudi.

Wata mata ta bayyana sirrin yadda kowa zai iya adana kudade, domin ita dai ta yi nata, ta yi wata dabara ta hanyar amfani da ambulam ta tara R50k (N1,290,634).

Kasancewar mutane da yawa na rayuwa ne kan albashin wata-wata, yana da matukar wahala ahali ya iya asusun kudi don gaba. Don haka, da yawan yaran zamani basu iya yin asusu ba.

Kara karanta wannan

Duk da Mahaifinta Yace Mummuna ce, Zata Aura Hamshakin Mai Arziki Bayan Aurenta 2 da Yara 7

Yadda kowa zai iya ajiyan N1m a shekara
Bidiyon Shawarin Wata Mata Na Yadda Mutane Zasu Iya Yin Asusun N1.2m a 2023 Ta Amfani da Ambulaf 100 | Hoto: TikTok / @nomazdiaries
Asali: UGC

Ta tara sama N1m a cikin ambulam guda 100

@nomazdiaries ta fito a kafar TikTok, inda ta yada bidiyon yadda ta yi amfani da ambulam guda 100, inda ta cika kowanne da kudi. Hakan ya ba ta daman tara kudaden da ta ambata; R50k.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kasancewar a cikin ambulam kudaden suke, kuma ta rarraba su, ya mata sauki wajen yin asusu ba tare da tunanin ajiye makudan kudade dumus a hannu ba a kowanne wata.

Ta ce ta saba da yin haka, kuma ya taimaka mata wajen warware lamurra masu yawa, ciki har da siyan mota, ta shawarci kowa ya gwada.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@Leo Queen:

“Na yi irin haka a shekarar da ta gabata, na tara R15k a karshen shekarar.”

@urbanmosadi:

“Ina son wannan tsarin. Ina bukatarsa. Nagode da kika koya mana.”

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

@Gillian Seetso:

“Na yi irin haka amma a sati nake cirewa na tsawon shekara sannan sai na kai banki inda nake samun riba yana ninka kansa.”

@ Nkuli:

“Tsarin ajiye kudi mai kyau.”

@Rethaaa-bileee:

“Watan Janairu na karatowa ‘yar uwa ina bukatar ambulam dinki.”

Dan Najeriya ya yi asusu, ya tara N5.5m

A wani labarin, wani dan Najeriya ya kwashi bagas yayin da ya fasa asusun da ya dauki lokaci yana tara kudi a ciki.

Bidiyon da muka samo ya nuna lokacin da mutumin ke kirga kudadensa, inda ya daure su dami-dami ya ajiye.

Kamar yadda aka gani a bidiyon, matashin ya tara kusan N5.5m, lamarin da yasa jama'a suka fara martani da cece-kuce a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.