Bukatu 6 da Muka Gabatarwa Buhari Sa'ilin da Muka Zauna da Shi Inji Aminu Daurawa
- Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun ba shugaban kasa shawarwari da nasihohi da suka zauna da shi
- Sheikh Daurawa yake cewa sun yi wa Muhammadu Buhari maganar tsaro da tattalin arzikin kasa
- Malaman sun nemi a kammala ayyukan da gwamnatin nan ta fara kafin cikar wa’adi a Mayun 2023
Abuja - Babban malamin musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana a kan haduwar da suka yi kwanaki da Mai girma Muhammadu Buhari.
Da ya zanta da gidan rediyon Freedom da ke garin Kano, Aminu Ibrahim Daurawa yace sun yi wa shugaban kasa nasihohi a lokacin da suka zanta da shi.
Malamin ya ce sun ba Muhammadu Buhari shawarwari kan yadda zai magance matsalolin kasa, ganin sun fi shi sanin halin da al’ummarsa suke ciki.
Shirin zaben 2023
A cewar Daura, sun tunatar da Buhari a kan maganar rashin tsaro da ake fama da shi da kuma sha’anin tattalin arziki, sannan sai maganar zabe mai zuwa.
Malaman sun nuna ya kamata a bada nasara ga duk wanda ya lashe zaben da za a shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A karasa ayyukan da aka fara
Aminiya a rahoton da ta fitar dazu, ta ce Malaman sun roki shugaban kasa alfarmar a karasa ayyukan da Gwamnatinsa ta fara kafin wa’adinsa ya kammala.
Daga cikin ayyukan nan akwai titin jirgin kasa da zai rika dauko mutane daga Kano zuwa Maradi, sannan akwai titin Abuja-Kano-Kaduna da aka fara tuni.
Shehin yake cewa sun batun danyen man da aka gano, suka ce zai yi kyau ayi maganin aukuwar rikici kan mallakar man tsakanin Bauchi da Gombe.
Ko da karasa wannan gagarumin aiki zai yi wahala, malaman su na so a iya gina matata a yankin.
Neman bashin Gwamnati
Wata magana da aka bijiro da ita a zaman ita ce batun bashin da irinsu bankin masana’antu da na cigaban kasa ke badawa, suka ce akwai gyara tsarin.
Rahoton ya nuna malaman sun koka da rashin ba 'Yan Arewa bashi saboda sharadin da aka bada na mallakar gida a Legas ko Abuja, wanda yana da wahala.
Malamai a Aso Rock
Shi ma shugaban kasa ya nuna ya ji dadin wannan taro da ya yi da masana addini, ya ce da ana yin haka, da an magance wasu matsalolin da ke damun kasar.
Karamin Ministan Ma’aikatar ayyuka, Hon. Umar Ibrahim El-Yakub ne ya yi wa malaman iso wajen shugaban kasar a fadarsa da ke Aso Villa a birnin Abuja.
Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya samu OON
Rahoto ya zo a baya cewa Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemu yana cikin manyan malaman addini da suka samu lambar girman OON daga gwamnati mai-ci.
Idan za a tuna, malamin ya aika wani amininsa, Alhaji Muhammad Bello Dalha ya karbi kyautar a madadinsa saboda bai iya zuwa garin Abuja a ranar bikin ba.
Asali: Legit.ng