Gwamnatin Najeriya Tayi Sabon Yunkurin da Ake sa ran Zai Kawo Karshen Wahalar Fetur
- Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya rage farashin da za a rika saidawa ‘yan kasuwa mai a sari
- A karshen wani zama da aka yi, an yarda ‘Yan kungiyar IPMAN su rika sayen mai a tasha kan N148
- Wannan matsaya da aka cin ma za ta sa ‘yan kasuwan su rage tsada, fetur ya rage tsaida a gidan mai
Abuja - A makon nan ne kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya dauki wasu matakan da ake ganin za su sa a samu man fetur a wadace a gidajen mai.
Vanguard a rahoton da ta fitar ranar Laraba, 14 ga watan Disamba 2022, ta ce a jiya kamfanin NNPCL ya rage farashin sayen fetur a tasha zuwa N148.
A dalilin rangwamen da kamfanin kasar ya yi, ana sa ran farashin litar man fetur ya sauka.
Baya ga rage farashin lita a manyan tashoshin mai, NNPCL ya yi alkawarin bada isasshen man da ake bukata ga‘yan kasuwa domin fetur ya samu sosai.
An gagara saida fetur a kan N170
Hakan na zuwa ne bayan ‘yan kasuwan sun koka da cewa kan N200 suke sayen duk litar man fetur daga tasoshin manyan ‘yan sarin da suke zaman kansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan tsadar ce ta jawo ‘yan kasuwa suka gagara cika umarnin da DSS ta bada kwanakin baya, ta bada umarni kowa ya rika saida litarsa a kan N170.
A zaman da aka yi a farkon makon nan, jaridar ta ce an yi nasarar shawo kan duk sabanin da ake da su tsakanin NNPLC da masu ruwa da tsaki a harkar.
Yadda muka yi da NNPCL - IPMAN
Wani babban jami’in gudanarwa na kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi ya tabbatar da wannan matsaya da aka cin ma, ya ce an yi masu rangwamen farashi.
Osatuyi yake cewa ‘yan kungiyarsu za su iya daukar fetur daga tasha a kan N148 a kowace lita, hakan zai sa su rage farashin da za su saida mai a kasuwa.
“An kyale ‘yan kungiyarmu (IPMAN) su dauki litar man fetur a kan N148, hakan yana nufin za mu iya rage farashinmu a gidajen mai.
A shirye muke mu hada-kai da sauran bangarori wajen shawo kan matsalar karancin mai a fadin kasar nan, ba tare da bata lokaci ba.”
- Mike Osatuyi
Yadda ake fama da tsadar fetur
Wani rahoto da mu ka fitar ya nuna samun fetur a kan N180 a gidajen mai ya gagara, kwanaki biyu bayan an yi alkawarin za a magance matsalar a Najeriya.
A jihohi da-dama a kasar nan, sai wanda yake da dace da doguwar kafa zai iya sayen fetur a farashi mai rahusa, kasuwar ‘yan bumburutu ta bude da kyau.
Asali: Legit.ng