Gobara Ta Tashi a Hedikwatar Tsaron Najeriya da Ke Babban Birnin Tarayya Abuja

Gobara Ta Tashi a Hedikwatar Tsaron Najeriya da Ke Babban Birnin Tarayya Abuja

  • An samu aukuwar wata 'yar gobara a babban birnin tarayya Abuja, ba a samu aikuwar wata asara ta rai ba
  • Rundunar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana yadda jami'ai suka yi nasarar shawo kan gobarar
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun gobara a hedkwatar tsaro ba, an sha samun hakan a lokuta da dama

Garki, Abuja - An samu Tashin wata gobara a hedkwatar tsaro ta Najeriya da ke a babban birnin tarayya Abuja a ranr Litinin 12 ga watan Disamba.

Wannan gobara dai ta tashi ne a hawa na biyu na hedkwatar, ya zuwa yanzu kuma ba a san musabbabin tashinta ba, Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa, jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya da sojojin da ke wurin sun yi kokari wajen ganin sun dakatar da yaduwar wutar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Asibitin Haihuwa, Sun Sace Jarirai

Daraktan yada labarai na tsaro a Najerya, Manjo Janar Jimmy Akpor ya tabbatar da faruwar lamarin.

Hedkwatar tsaro ta kama da wuta
Gobara Ta Tashi a Hedikwatar Tsaron Najeriya da Ke Babban Birnin Tarayya Abuja | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda gobarar ta faru da yadda aka shawo kanta

Ya kara da cewa, an yi nasarar kashe wutar kuma an tattara dukkan ma’aikatan da ke cikin ginin, rahoton Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa:

"An samu tashin wuta kadan a hawa na biyu na hedkwatar tsari da ke Garki Abuja da yammacin 12 ga watan Disamba 2022. Ba a san musabbabin tashin gobarar ba ya zuwa yanzu.
"Sai dai, an shawo kan lamarin ta hanyar hadin gwiwa da kokarin jami'an soji da na hukumar kashe gobara ta tarayya. Dukkan jami'ai da ma'aikata fararen hula an tattara su ba tare da wani rauni ko rasa rai ba.
"Hakazalika, komai ya daidaita. An fara binciken musabbabin tashin gobarar nan take."Mun godewa hukumar kashe gobara ta tarayya da sauran jama'ar gari baki daya bisa ci gaba da ba da goyon baya da fatan alheri ga rundunar tsaron Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

A baya an taba yin gobara a hedkwatar tsaro

Ba wannan ne karon farko da gobara ta kama a hedkwatar tsaron Najeriya, an yu hakan a watan Maris din shekarar 2021 da ta gabata.

A wancan lokacin, hukumar tsaron kasar nan ta bayyana yadda lamarin ya faru tare da yin karin haske ga jama'ar kasa.

Yana daga abubuwan da ake yawan samu a Najeriya, gobara a ofisoshin gwamnati, hakan na dasa ayar tambaya a zukatan 'yan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.