Da dumi-dumi: Gobara ta kama hedkwatar sojojin Najeriya

Da dumi-dumi: Gobara ta kama hedkwatar sojojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta bayar da rahoton wata gobara da ta barke a babban ofishinta da ke Abuja.

An danganta abin da ya haddasa wutar da matsalar wutan r lantarki.

A cewar wata sanarwa daga Daraktan hulda da jama’a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima: “Matsalar wutar lantarki ne ya haifar da wata karamar gobara a Hedikwatar Sojoji dake Abuja da safiyar ranar Talata.

“Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 10:15 na safe ya kasance ne sakamakon karamar matsalar wutan lantarki a daya daga cikin ofisoshin.

“Ginin Hedikwatar Soja a yanzu haka tana kan wasu gyare-gyare da suka hada da aikin gyaran wutan lantarki.

“Tun a lokacin da gobarar ta tashi ma’aikatar kashe gobara ta sojojin Najeriya ta kashe wutar. Babu wani wanda aka yi asara a yayin faruwar lamarin kuma tuni kowa ya koma kan aikinsa ”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel