Ana Shirin Zaben 2023, Tsageru Sun Cinna Wa Ofishin INEC Wuta A Fitacciyar Jihar Kudancin Najeriya

Ana Shirin Zaben 2023, Tsageru Sun Cinna Wa Ofishin INEC Wuta A Fitacciyar Jihar Kudancin Najeriya

  • Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun sake kai hari ofishin hukumar INEC da jihar Imo sun kona ofishin
  • Maharan kuma sun sace mutane uku cikin magina bakwai da ke aikin gyaran ofishin na INEC, amma daga baya sun sako su
  • Kwamishinan hukumar INEC na jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu ya koka kan hare-haren da aka kaiwa ofisoshin hukumar

Jihar Imo - An cinna wa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ta karamar hukumar Orlu, jihar Imo wuta, rahoton Daily Trust.

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan an kona ofishin hukumar da ke jihar Ebonyi, inda aka lalata kayan zabe da suka hada da akwatuna.

Taswirar Imo
Ana Shirin Zaben 2023, Tsageru Sun Kona Ofishin INEC A Imo. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Da ya ke tsokaci kan harin, kwamishinan hukumar kuma ciyaman na kwamitin wayar da kan masu zabe, Festus Keyamo, ya ce lamarin ya faru a karamar hukumar Orlu.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin sanarwar da ya fitar, kwamishinan zabe na jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ya bada rahoto kan harin.

Okoye ya ce:

"Ginin wanda ake yin gyara sosai biyo bayan harin da aka kai a baya, an lalata shi tare da kona wani bangare. An sace uku cikin magina bakwai da ke aikia wurin amma daga baya aka sake su.
"Ba domin rundunar yan sandan Najeriya da suka turo da jami'ansu cikin gaggawa ba da asarar da za a yi ya fi hakan."

Hare-haren da aka kai wa ofisoshin INEC yana wuce gona da iri - Uchenna

Ya koka kan cewa hare-haren ya fara yawa.

Ya kara da cewa:

"Hukumar ta kuma sake nuna damuwarta kan yawaita hare-haren da ake kai wa ofisoshinta da matsalar da hakan zai yi ga babban zaben 2023."

Kara karanta wannan

Shugaban Kwastam ya Sanar da Muhimmin Dalilin Kama Kayan Chana da Suka yi a Najeriya

Hare-haren da ake kai wa ofisoshin INEC ba zai hana yin zabe ba

A bangare guda, hukumar INEC a baya-bayan nan ta ce hare-haren da ake kai wa ofisoshinta ba zai hana yin babban zaben shekarar 2023 ba.

Mahmood Yakubu, shugaban INEC na kasa ya ce:

"Za mu cigaba da aiki tare da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa an samar da tsaro a ofisoshinmu da kare ma'aikatanmu.
"Muna son nuna damuwarmu kan hare-haren da aka kai wa ofisoshinmu, amma hakan ba zai hana hukumar yin zabe kamar yadda aka shirya yi ba."

Ofishin INEC Ta Jihar Imo Ta Yi Gobara

Gobara ta tashi a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na garin Orlu da ke jihar Imo a ranar 3 ga watan Fabarairu.

Kamar yadda da The Sun ta rahoto, gobarar ta tashi ne misalin karfe 6 na asuba a wani daji da ke kusa da ofishin a karamar hukumar Orlu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel