Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

  • Gwamnan CBN ya fito da tsarin da zai hana a iya cire kudi da yawa a bankuna, ATM da POS a Najeriya
  • Peoples Democratic Party, Social Democratic Party, da Africa Democratic Congress sun yi tir da sabon tsarin
  • Jam’iyyun adawa da-dama sun tafi a kan tsarin zai kawowa mutanen da ke rayuwa a karkara matsala

Abuja – Wasu jam’iyyun siyasa ba su goyon bayan sabon tsarin da babban bankin kasa ya kawo na rage adadin kudin da za a rika cirewa daga bankuna.

Wani rahoto da ya fito daga Punch, ya nuna jam’iyyun hamayya irinsu PDP, ADC, ADP da kuma SDP ba su goyon bayan tsarin da bankin CBN zai dabbaka.

Jam’iyyun su na ganin a takaita kudin da za a iya cirewa a rana ko a mako, zai kawo cikas wajen samun dukiyar da za ayi amfani da su wajen yakin zabe.

Kara karanta wannan

A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

Sauran jam’iyyu kamar AAA, SLP da APGA sun tattauna da jaridar a mabanbantan lokuta, kuma su na sukar matakin nan da Godwin Emefiele ya dauka.

Jam'iyyar PDP ta koka

Dele Momodu wanda jagora ne a PDP yace idan tsarin ya fara aiki, zai taba kamfe na jam’iyyu, kuma zai kawo duk wata jam’iyyar siyasa kalubale a 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Momodu wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa yace babu yadda ‘yan takara za su samu isassun kudin da suke nema domin su iya lashe zabe a haka.

Atiku
Atiku yana kamfe a Abuja Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Ba ayi tunani ba

Jam’iyyar PDP tana ganin dokar za ta kuntatawa jama’a, Momodu yake cewa Gwamnan CBN ya fito da wannan tsari ba tare da yin zurfin nazari ba.

Sakataren yada labaran SDP na kasa, Alpha Muhammed yana da irin wannan ra’ayi, yace an fito da dokar da kwatsam za ta kawo matsala a wajen zabe.

Kara karanta wannan

2023: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Gana da Gwamnan Tsagin Wike, Bayanai Sun Fito

Muhammed yace dole a bukaci kudi wajen harkar zabe, a dalilin haka tsarin zai yi tasiri mummunan tasiri a 2023, amma hakan ya sabawa ra'ayin CNPP.

Sani Yabagi wanda shi ne shugaban jam’iyya na kasa kuma mai neman takarar shugaban kasa a ADP yace za a rasa kudin kamfe idan aka fito da tsarin.

Amma tsarin zai taimaka wajen rage sayen kuri’un jama’a a wajen zabe, sai dai a wajen hakan, Yabagi yace za a rasa kudin da za ayi dawainiyar takara.

NNPP da siyasar Kano

A lokacin da ake zargin iyalan Gwamnan Kano mai-ci da katsalandan a harkar mulki, an samu rahoto Abba Gida-Gida yace ba za ayi haka a mulkinsa ba.

Idan Abba Kabiru Yusuf da NNPP suka karbi Gwamnatin jihar Kano a zaben 2023, za a soke ofishin uwargidar Gwamna, kuma za a daina cinye kudin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng