Yadda Mutane Ke Fakin Motocinsu Masu Tsada a Bakin Gidan Cin Abinci Don Su Kwashi Tuwo

Yadda Mutane Ke Fakin Motocinsu Masu Tsada a Bakin Gidan Cin Abinci Don Su Kwashi Tuwo

  • Wani bidiyon gidan cin abinci a bakin hanya, inda manyan mutane ke zuwa da manyan motoci domin siyan tuwo ya yadu a intanet
  • An ga lokacin da mutane da yawa a bakin gidan cin abincin suna jiran layi, wasu kuwa suna kwasar girki mai dadi
  • Jama'ar soshiyal midiya sun yi mamaki, sun kuma bayyana bukatar sanin dalilin da yasa mutane ke tururuwa a wurin

Wani mutum, @mr.korkorte, ya yada wani bidiyon gidan cin abinci da ke da kwastomomi masu matukar ban mamaki, mutane suka ce abincin wurin zai yi matukar dadi.

A cikin gajeren bidiyon da ya yada a TikTok, ya dauki bidiyon manyan motoci irinsu Bently da kwatsomomi suka faka domin cika cikinsu da tuwo.

Ba wani gidan cin abinci bane na a zo a gani, gama gari ne da aka gina da katako da kwano a gefen hanya. An kuma zagaye shi ne da kujerun zama na katako.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

Gidan tuwon da attajirai ke layi don cin tuwo
Yadda Mutane Ke Fakin Motocinsu Masu Tsada a Bakin Gidan Cin Abinci Don Su Kwashi Tuwo | Hoto: TIkTok/@mr.korkorte
Asali: UGC

An ga mutane da yawa yayin da suke layin siyan tuwo a gidan cin abincin, wasu kuma suna gefe suna kwasar tuwo; hannu baka hannu kwarya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'ar TikTok sun shiga mamaki, suna bukatar sanin wannan wani wuri ne haka don su ma su je su dandana dadin tuwon da ake siyarwa.

Wanda ya yada bidiyon ya ce wannan gidan siyar da abinci dai a birnin Accra yake a kasar Ghana.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a a shafin sada zumunta

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutane 200 ne suka yi martani ga bidiyon, mutum 13,000 kuwa sun yi dangwalen nuna sha'awarsu.

Ga dai kadan daga martanin jama'a kamar yadda muka tattaro daga sashen sharhin TikTok:

Nobody yace:

"Bidiyo na hudu na tuwo da nake gani kenan, shin yau kam ranar tuwo ce ta duniya?"

prettypearl1251 tace:

Kara karanta wannan

Matashin Miloniya Ya Baje Kolin Hadadden Gidansa da Tsadaddiyar Motar Benz, Bidiyon Ya Yadu

"Ya kamata ku fada mana a ina ne ai ko"

Ola Godson231 yace:

"Idan ban ce ganin abincin nan ya sa na fara jin yuwa ba me zan ce, wayyo Allah na."

Igbo Royalties yace:

"Ku ci gaba da aiki mai kyau! Aikinku na kyau."

mzz_boss_ yace:

"Gidan tuwo mafi araha kenan ya zuwa yanzu!"

Adina From Textured yace:

"Zan gwada siya. Wurin ya yi min kyau."

Dudumayana yace:

"Gidan tuwo ne nan ko kuma gidan tsafi."

Hairby_matib yace:

"Abincin Ghana...kamar bai dahu ba, amma tabbas zai yi dadi."

motunrayo1824 yace:

"Shin wannan a Legas ne don Allah?"

Wata kungiya ta shawarci Buhari ya kakaba haraji kan lemun kwalba

Daga cin abinci sai kuma neman abin sha ko? Gwamnatin Najeriya na shirin kakaba haraji kan kayan kwalba da ba sa bugarwa saboda wasu dalilai.

Wata kungiya ta ce abin da gwamnati ta tsara daidai ne, kuma wannan zai taimaka wajen rage yaduwar cututtuka masu alaka da zuciya da suga.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Hakazalika, maganar sanya harajin ya kawo batun karin farashi ga wadannan kayayyaki, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.