Gwamnan CBN Ya Hadu da Shugaban Kasa, Ya Yi Maganar Janye Dokar Kayyade Kudi
- Godwin Emefiele yace ba za a fasa aiwatar da tsarin da zai takaita kudin da za a iya cirewa a banki ba
- Gwamnan babban bankin kasar ya yi wa shugaban kasa bayanin inda aka kwana a kan wannan shiri
- Kudi ba su komawa banki don haka Emefiele yake ganin ya zama dole ga bankin CBN ya dauki mataki
Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele ya nuna babu yiwuwar watsi da aiwatar da dokar da aka kawo na takaita cire kudi.
Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba 2022, Godwin Emefiele zai bayyana gaban ‘yan majalisar tarayya kan tsarin da ya kawo.
Emefiele yake cewa daga lokacin da CBN ya fara shigo da tsarin watsi da takardun kudi a 2012, an fito da kafofin yanar gizo da na zamani na yin hada-hada.
Gwamnan babban bankin yake cewa tun tuni ya kamata a tabbatar da aiwatar da tsarin, amma sai aka dakata domin kafofin da ake da su, su watsu sosai.
Rahoton yace da ya zauna da Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari, Emefiele ya shaidawa shugaban kasa shirin aiwatar da tsarin yana tafiya da kyau.
Bayan ya hadu da shugaban kasa, Gwamnan ya shaidawa manema labaran da ke fadar Aso Villa a birnin Abuja cewa dole za a aiwatar da wannan tsari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za mu zauna da 'Yan majalisa - CBN
Lokaci bayan lokaci, Gwamnan na CBN yace za su rika sanar da ‘yan majalisar tarayya inda aka kwana, tun da an nemi bayani, za su je su gamsar da su.
Babu ta yadda za a yi a cigaba da tafiya a haka, Emefiele yace kudin da suke yawo a gari sun zarce kudin da ke bankuna, don haka ne suka kawo sabon tsarin.
CBN za ta rika duba wannan tsari bayan lokaci domin ganin matakin da za a dauka.
Sababbin kudi sun fara fitowa
A game da batun canza manyan takardun kudi kuwa, Emefiele yake cewa a ranar Larabar nan bankuna sun fara rabawa mutane sababbin kudin da aka buga.
Mista Emefiele yace mutane su kwantar da hankalinsu, sababbin takardun kudin za su zagaya, sannan za a iya amfani da tsofaffin kudin har karshen Junairu.
A cikin ba’a, Gwamnan yace za a a cigaba da kashe duka bugun kudin tare. Vanguard tace zuwa yanzu an iya dawo da Naira Tiriliyan 1 cikin asusun bankuna.
'Yan majalisa ba su gamsu ba
An ji labari ‘Yan majalisar wakilai suna ganin bai kamata tsarin takaita cire kudi ya yi aiki ba, don haka Gwamnan banki zai yi masu bayanin amfanin tsarin.
Majalisar kasar ta bukaci CBN ta dakatar da tabbatar da tsare-tsaren nan, sannan Gwamnan ya gurfana a gabanta a mako mai zuwa domin amsa tambayoyi.
Asali: Legit.ng