Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN ta Dakatar da Tabbatar da Sabbin Tsarikan

Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN ta Dakatar da Tabbatar da Sabbin Tsarikan

  • Majalisar wakilan Najeriya a ranar Alhamis ta hautsine da cece-kuce daga mambobinta kan sabbin tsarikan kayyade kudin cirewa a kowacce ranar daga banki
  • Majalisar ta bukaci CBN ta dakatar da tabbatar da tsarikan nan sannan Gwamnan bankin ya gurfana a gabanta a mako mai zuwa don amsa tambayoyi
  • ’Yan majalisar sun ayyana cewa, Za a durkusar da masu kananan sana’o’i da mazauna kauye wadanda basa ta’ammali da banki

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya ya dakatar da tabbatar da sabbin tsarikan hana yawon tsabar kudi da za a fara a ranar 9 ga Janairun 2023 har zuwa lokacin da zuwa wani lokaci.

Majalisar
Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN ta Dakatar da Tabbatar da Sabbin Tsarikan. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Majalisar tayi kiran gaggawa ga Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele kamar yadda tanadin dokokin babban bankin suka nuna domin bayani ga majalisar kan sauran tsarikan bankin na baya-bayan nan, kamar yadda shafin majalisar wakilan na Twitter ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kafa tarihi: Za a yi wani babban taro a Amurka, an gayyaci Buhari da wasu shugabanni 48 na Afrika

‘Yan majalisar wakilan sun matukar fusata a ranar Alhamis yayin da mambobin suka dinga kushe sabon tsarin inda suka ce zai matukar shafar kananan kasuwanci da tattalin arziki tunda yankunan karkara basu iya samun bankuna.

Sai dai, bayan ‘dan majalisa Mark Gbillah ya tada batun tanadin babban bankin, majalisar tayi umarnin ganin gwamnan babban bankin a ranar Alhamis, 15 Disamban 2022 domin yayi bayani kan dokokin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanda ya mika bukatar, Magaji Da’u Aliyu, yace sabbin tsarikan wadanda suka takaita cire N20,000 a kowacce rana bai dace a bar shi ba saboda illar da zai yi ga ‘yan Najeriya ballantana masu kananan kasuwanci.

Yace yayin da kasar ke kokarin daidaitawa da hukuncin sake fasalin Naira, CBN tana kokarin kawo wani tsari da zai yi matukar illa ga talakawa ba tare da an duba shi da kyau ba.

Kara karanta wannan

APC Yobe: Bayan Lallasa Lawan a Kotu, Machina ya Magantu a Karo na Farko

Babban bankin Najeriya ta saki sabbin tsarikan hada-hadar kudi

A wani labari na daban, babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar wasu sabbin tsarikan hada-hadar kudade a kasar nan wanda zasu fara aiki a ranar 9 ga Janairun 2023.

Daga cikin tsarikan akwai kayyade kudin da mutum zai cire a kowacce rana ko kuma kungiyoyi da kuma takardun kudin da za a dinga zubawa a ATM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel