Budurwa ta Durkusa Guiwa Bibbiyu Gaban ‘Dan Uwanta da Ya Saki Karatu Saboda Ta Kammala Nata

Budurwa ta Durkusa Guiwa Bibbiyu Gaban ‘Dan Uwanta da Ya Saki Karatu Saboda Ta Kammala Nata

  • Wata matashiyar budurwa ta kammala karatu a jami’a amma ta saka wa ‘dan uwanta rigar shaidar gamawa ta durkusa kuma gaban shi
  • Budurwar mai shekaru 27 cike da godiya da farin ciki ta nuna jin dadinta kan yadda ‘dan uwantan ya hakura da karatunsa don ta kammala nata
  • Jama’a da yawa sun yabawa ‘dan uwan budurwar kan yadda ya saka bukatar ‘yar uwarsa a gaba kuma hakan ya haifar da abinda ake bukata

Ba iyalai masu tarin yawa bane ke iya saka yaransu duka a makaranta ba saboda matsin rayuwa da rashin kudi.

Budurwa a gaban ‘Dan uwanta
Budurwa ta Durkusa Guiwa Bibbiyu Gaban ‘Dan Uwanta da Ya Saki Karatu Saboda Ta Kammala Nata. Hoto daga chnitakotchasit.
Asali: UGC

Wasu daga cikin yaran kan sadaukar da karatin su domin su bai wa ‘yan uwansu damar zuwa makaranta ta yadda a gaba zasu iya inganta rayuwarsu baki daya.

Wata budurwa wacce ke cike da murna ta kawata ‘dan uwanta da rigar shaidar kammala karatun ta a ranar da ake yaye su a makaranta.

Tsananin girmamawa da godiya

Daga nan ta zube kasa guiwa bibbiyu tare da gurfana a gaban shi a matsayin alamar godiya kan sadaukarwar da yayi saboda ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan karramawa ce daga budurwar ‘yar asalin kasar Thailand wacce ke nuna alamar girmamawa a al’adarsu kuma bata ji kunyar yin hakan ba a gaban kowa.

‘Dan uwantan dake tsaye ya taba kan budurwar domin nuna mata kauna a bidiyo.

Budurwar ta kammala karatu ne daga jami’ar Rajabhat dake kudancin Thai a NakhonSri Thammarat.

Rayuwa suke tare da ‘dan uwanta da kuma mahaifiyarsu dake fafutuka

Tana rayuwa ne da ‘dan uwanta tare da mahaifiyarsu inda mahaifiyar ke fafutuka wurin ganin ta ciyar dasu da ilimantar dasu.

Hakan ne yasa mahaifiyarsu ta cire ‘dan uwan daga makaranta ta yadda budurwar zata samu ta cigaba da karatu.

Matashin bai fahimci hakan ba har sai da ta kammala karatun ta na jami’a yayin da shi kuma bai je ko ina ba.

Mahaifiyarsu ce bata iya biyan kudin makarantarsu baki daya don haka ta sadaukar da ilimin yaro namijin domin macen ta samu.

Soshiyal midiya tayi martani

Tuni jama’a suka dinga tsokacin tare da yabawa matashin kan yadda ya sadaukar da sashin rayuwarsa domin ‘yar uwarsa.

Dolphinecare:

“Mutane na daban a rayuwar nan sun cancanci a yaba musu. Daga Singapore nake kallon wanna lamari. Ya dace duniya ta ga wannan. Sau da yawa a tattare da nasarar ka akwai wani bayani.”

Nisan Dhom Nauzder Niduila:

“Wayyo Allah, hawaye ne ke zuba daga idanuwa na. Dukkan ku kun hadu, ‘yan uwa masoyan juna masu son farin cikin juna.”

Shane Espergal yace:

“Ina taya ku murna. Ubangiji ya saka muku albarka. Na yaba miki kan yadda ki ka mutunta ‘dan uwan ki. Kin kyauta ‘yar uwa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel