Sojoji Na Fuskantar Matsin Lamba Don Yin Katsalandan A Zabe, Babban Hafsan Tsaro Na Najeriya

Sojoji Na Fuskantar Matsin Lamba Don Yin Katsalandan A Zabe, Babban Hafsan Tsaro Na Najeriya

  • Babban hafsan sojoji kasan Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce ana yi sojoji matsin lamba su kawo cikas ga zaben 2023
  • Sai dai shugaban sojojin ya ce ba za su amince da hakan ba za su cigaba da yin ayyukansu ba tare da nuna bangaranci ba kamar yadda Shugaba Buhari ya umurta
  • Irabor ya kuma ce rundunar sojojin na Najeriya tana bawa jami'anta da dakaru horasawa na musamman dangane da aikin zabe

FCT, Abuja - Janar Lucky Iraba, Babban Hafsan Tsaro Na Najeriya, CDS, ya ce rundunar soja na fuskantar matsin lamba don yin katsalandan a babban zaben shekarar 2023, rahoton The Punch.

Shugaban sojan, amma ya ce rundunar sojojin za ta cigaba da aikinta ba tare da nuna bangaranci ba kuma za ta taimakawa rundunar yan sanda don sa ido tare da bada tsaro don zabe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Lucky Irabor.
Sojoji Na Fuskantar Matsin Lamba Don Yin Katsalandan A Zabe, Babban Hafsan Tsaro Na Najeriya. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Irabor ya yi magana ne a ranar Alhamis yayin taron manema labarai da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a fadar villa da ke Abuja, The Cable ta rahoto.

Sojoji za su bi umurnin Shugaba Buhari na rashin nuna bangaranci - Irabor

Shugaban tsaron ya tabbatar da cewa sojojin ba yan siyasa bane, yana mai cewa ana saka matakai da suka dace don tabbatar an bi umurnin Shugaba Muhammadu Buhari na rashin nuna bangaranci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an bawa jami'an sojojin horaswa na yin aiki a matsayin kwararru sannan an sanar da su dokokin aiki kafin, yayin da bayan zabe.

Irabor: Ana bawa sojoji horasawa na musamman kan aikin zabe

Irabor ya kara da cewa kuma ana bawa jami'ai da dakarun sojojin horaswa ta musamman kan ayyukan zabe.

Ya yi magana kan nasarorin da rundunar sojin ta samu don samar da tsaro a kasa ciki har da tura su sassa daban-daban na hukumomin tsaro, don dakile yan tada kayan baya, yan ta'adda da satar danyen mai.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Bayyana Abubuwan da Zai Tunkara a Ranar da Ya Fara Shiga Fadar Aso Rock

Sojoji sun ceto fiye da mutum 300,000 daga hannun yan ta'adda

Irabor ya ce an ceto fiye da mutane 300,000 daga wurin wadanda suka sace su tun 2014 sannan yan gudun hijira da suka bar garuruwansu sun fara komawa.

CDS din kuma ya ce tsaffin yan ta'adda da a yanzu ake bawa horaswa, za a yaye su a Fabrairun 2023.

Za a kori duk wani sojan da ba a gama yarda da imaninsa ba a Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya na shirin yin ritaya ga duk wani jami'in soja da ke raba kafa wurin biyayya ga kasa.

Wadanda za a sallama sun kunshi wadanda ba su cikakkiyar biyayya ga hukuma da suke cike da fushi a rundunar sojin ruwa, sama da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164