Ana shirin yin waje da duk wani Sojan da ba a gama yarda da imaninsa ba a Najeriya

Ana shirin yin waje da duk wani Sojan da ba a gama yarda da imaninsa ba a Najeriya

  • Hedikwatar tsaro ta bada umarnin a sallami duka sojojin da ake tunanin ba su da cikakkiyar da’a
  • Sabon umarnin zai shafi sojojin ruwa, sojojin sama da sojojin kasa da suka raba kafa wajen da’a
  • Akwai masu ganin bai dace a kori jami’an tsaro a lokacin da ake fama da karancin ma’aikata ba

Abuja - Ana shirin yi wa jami’ai da-dama ritaya daga gidan soja bayan umarnin da manya suka bada na sallamar wadanda suka raba kafa a wajen biyayya.

Daily Trust ta rahoto cewa za a kori marasa cikakkiyar da’a ga hukuma da kuma wadanda suke cike da fushi a rundunar sojojin sama, da kasa da na ruwa.

Rahoton ya ce wannan bayani ya fito ne daga wata takarda wanda Rear Admiral Muhammed Nagenu ya sa wa hannu a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni 2022.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

Rear Admiral Muhammed Nagenu ya fitar da takardar ne a madadin shugaban hafsun tsaro na kasa baki daya, Janar Lucky Irabor, a kan halin da sojoji su ke ciki.

Janar Lucky Irabor yana ganin cewa jami’an tsaron da ba su da cikakkiyar biyayya da masu jin haushin hukuma ba su da ragowar amfani wajen sha’anin tsaro.

A dalilin haka, aka bukaci a daina aiki da irin wadannan sojoji, domin za su iya dawo da hannun agogo baya. Sanarwar ta nemi ayi masu ritaya yadda doka ta ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji
Manyan Hafsun Sojoji Hoto: @NigerianArmy
Asali: Facebook

Jaridar ta ce babu tabbacin ko wadannan sojoji da ake magana sun nemi su yi juyin mulki ne ko yunkurin cin amanar kasa, asali ma ba a fahimci wa ake nufi ba.

Dalilin bada wannan umarni - DHQ

Darektan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor yake cewa dalilin daukar wannan mataki shi ne a tabbatar da ladabi da biyayya a gidan soja.

Kara karanta wannan

Jami’an Sojoji sun kama wata mota dankare da kayan makamai makil a Najeriya

Janar Jimmy Akpor bai bayyanawa ‘yan jarida adadin wadanda umarnin zai shafa ba. A cewarsa babu wasu takamaimen jami’an da ake hari da wannan umarni.

Ba daidai ba ne inji Tsohon Kanal

Wani tsohon jami’in soja, Amb. (Dr) Okhidievbie Roy ya shaidawa manema labarai cewa hakan ba daidai ba ne, kuma zai kara jefa sha’anin tsaro a cikin hadari ne.

Okhidievbie Roy wanda shi ne Sakataren kungiyar REMENAF ta tsofaffin sojoji, ya ce yi wa wasu jami’ai ritaya yana nufin za a samu karin karancin jami’an tsaro.

An kama mota da makamai

Ku na da labari cewa Rundunar sojojin Najeriya sun ce sun ci karo da wata mota da ta kinkimo tulin miyagun makamai. Wannan abin ya faru ne a jihar Kuros Riba.

Motar ta biyo ta gaban Dakarun Sojoji don haka aka nemi a tsaida direban, amma ya ki tsayawa. Da aka bincika sai ga shi ta dauko bama-bamai, harsahi da khakin sojoji.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Asali: Legit.ng

Online view pixel