Mun Shafe Shekaru 9 Tare: Matashiya Mai Digiri Uku Ta Biya Sadakinta Da Kanta, Ta Auri Sahibinta

Mun Shafe Shekaru 9 Tare: Matashiya Mai Digiri Uku Ta Biya Sadakinta Da Kanta, Ta Auri Sahibinta

  • Wata matashiya ta yi amfani da kudinta wajen biyan sadakin aurenta maimakon barma mijinta kamar yadda al'ada ta tanadar
  • Matashiyar mai shekaru 34 kuma mai digiri guda uku ta ce ta fi mijinta samun kudi saboda haka ta yanke shawarar taimaka masa
  • Da fari mijin ya yi adawa da lamarin amma daga bisani ya yarda da tsarin sannan ya bar sahibarsa ta biya sadakin

Wata matashiyar mata wacce ta biya kudin sadakinta da kanta ta ba da labarin lamarin.

Matar mai shekaru 34 mai suna Zuku ta kasance mai digiri uku kuma iyayenta sun sha alwashin karbar kudade masu yawa daga wajen mijinta.

Mace da namiji
Mun Shafe Shekaru 9 Tare: Matashiya Mai Digiri Uku Ta Biya Sadakinta Da Kanta, Ta Auri Sahibinta Hoto: Klaus Vedfelt and Pollyana Ventura/Getty Images
Asali: Getty Images

Da take bayar da labarin a News24, Zuku ta ce ita da kanta ta shirya batun biyan sadakinta da kanta.

Kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda Allah ya sauya jinsin jaririn wata mata daga mace zuwa namiji ya ba da mamaki

"Idan da ace wani ya fada mani cewa a shekaru 34 zan biya sadaki na, da na yi dariya. Amma eh, hakan ya faru - na biya sadakina, ba zan yi karya ba, da fari na ji kunya."

A al'adar Afrika, hakkin ango ne ya biya sadakin amarya ba wai ita ta biya ba.

Amma Zuku ta ce tana karbar albashi fiye da na sahibinta don haka ta yanke shawarar tallafa masa wajen biyan sadakin.

Mun shafe shekaru 9 muna soyayya, cewar Zuku

Kafin su yanke shawarar yin aure, Zuku ta ce sun shafe shekaru tara suna soyayya da mijinta.

Da ta zo da batun biyan sadakinta, da farko angon nata ya ki yarda amma daga bisani ya amince da taimakon.

Zuku ta ci gaba da labarinta

"Mijina bai goyi bayan lamarin ba sannan ya ki amincewa da bukatata, amma hakan ya yi ma'ana sosai. Danginsa za su biya kudi da yawa na bukukuwan auren da yiwa dangina kyauta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mawaki D’banj ya Shiga Hannun ICPC Kan Zargin Damfarar Miliyoyin N-Power

"Kuma ina samun kudi fiye da shi sannan ina a matsayin gabatar da kudin sadakin. A wannan lokacin ya ji kamar an tauye shu amma a zahiri, hakan ya fi mana mu dukka da kuma rayuwar da muke shirin ginawa tare."

Ango ya yi dambe da wani da ya halarci shagalin bikinsa

A wani labarin, an ba hammata iska tsakanin wani ango da dan gayya wanda yayi kokarin lika masa kudi yayin da suke rausayawa da amaryarsa a filin rawa.

Mutumin ya yi masa liki na farko amma angon ya cire ya wurgar sai ya sake komawa a karo na biyu lamarin da ya arzuka shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng