Kasar Guinea Bissau Ta Karrama Buhari da Babbar Karramawar Kasa

Kasar Guinea Bissau Ta Karrama Buhari da Babbar Karramawar Kasa

  • Kasar Guinea Bissau ta karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya duba da irin ayyukan siyasa da ya gudanar a kasar nan
  • Shugaba Buhari ya kai ziyara kasar ne da ke nahiyar Afrika, inda aka sanyawa wani titi sunansa
  • Jamhuriyar Nijar ta yi irin wannan karramawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wannan shekarar

Kasar Guinea Bissau - Jamhuriyar Guinea Bissau a ranar Laraba ta karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya bisa gudunmawar da ya bayar a ci gaban siyasa a Afrika ta Yamma.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, inda yace wannan karramawa abin alfahari ne Najeriya.

Hakazalika, sanarwar da kasar ta Guinea Bissau ta fitar ta bayyana cewa, an karrama Buhari ta hanyar sanyawa wani titin da aka kaddamar a kasar sunansa.

Kara karanta wannan

Buhari Zai Garzaya Guinea Bissau, Za a Karrama Shi da Lambar Yabo Mafi Daraja ta Kasar

Yadda aka karrama Buhari a kasar waje
Kasar Guinea Bissau ta karrama Buhari da babbar karramawar kasa | Hoto: @USEmbalo
Asali: Twitter

Umaro Sissolo Embalo, shugaban kasa Guinea Bissau ya yada hotunansa tare da Buhari a lokacin da suka hadu a kasar a yau Laraba 7 ga watan Disamba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari ya karbi karramawar da aka yi masa

A hotunan da ya yada, an ga lokacin da shugaba Buhari ke karbar lambar karramawar da kuma sadda yake magana da shugaban kasar.

Embalo ya rubuta da harshen Faransancin cewa:

“Babban abin alfahari da na karbi bakuncin shugaban kasa @Mbuhari a ziyarar aiki da ya kawo Bissau. Duba da yadda yake tafiyar da shugabancinsa, an karrama shugaban kasa @Mbuhari da babbar karramawa kuma an sanyawa wani titin da aka kaddamar sunansa.”

Akwai dankon zumunci da alaka mai karfi tsakanin kasashen Afrika, shugaba Buhari na shan yabo daga shugabanni.

Nijar ta sanyawa titi sunan shugaba Buhari saboda gudunmawar da ya bayar a Afrika

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari Ya Yi Kwanaki fiye da 200 a Asibiti, Ya Ziyarci Kasashe 40

Girmamawar da Nijar ke yiwa shugaban kasa Muhammadu na Najeriya yasa kasar ta sanyawa titi sukutun sunansa a wata karramawa da ta yi masa.

Rahoto ya bayyana cewa, Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya ce a birnin Niamey ne aka zabi wani titi tare sanya masa sunan Buhari.

An bayyana karrama Buhari ne jim kadan bayan da ya kaddamar da titin a wata ziyara da ya kai kasar kwanakin baya kadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel