Buhari zai Shilla Guinea Bissau, Za a Karrama Shi da Lambar Yabo Mafi Daraja

Buhari zai Shilla Guinea Bissau, Za a Karrama Shi da Lambar Yabo Mafi Daraja

  • A ranar Laraba mai zuwa Shugaba Buhari zai dire kasar Guinea Bissau domin amsa gayyatar Shugaba Umaro Sissalo na kasar
  • Za a yi shagalin bikin kwana daya a fadar shugaban kasan inda za a karrama Buhari da lambar yabo mafi daraja ta kasar
  • Baya ga haka, za a kaddamar da titi a babban birnin jihar inda za a kara da bayyana nasarorin shugaban kasan wurin hada kan Afrika ta kudu

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba zai shilla kasar Guinea Bissau inda za a karrama shi da lambar yabo.

Buhari zai shilla Guinea Bissau
Buhari zai Shilla Guinea Bissau, Za a Karrama Shi da Lambar Yabo Mafi Daraja. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Lambar yabon da za a kawata shi da ita a Bissau sun ce zata kasance mafi girma ta kasar sakamakon gudumawar da ya bayar wurin kawo daidaituwar siyasa a kasashen Afrika na yamma.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari Ya Yi Kwanaki fiye da 200 a Asibiti, Ya Ziyarci Kasashe 40

Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka fitar ranar Talata ta hannun mai bai wa shugaban kasan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Buhari zai amsa gayyatar shugaban kasan Guinea Bissau, Umaro Sissolo Embalo kan biki na musamman da za a yi a fadarsa wanda zai hada da kaddamar da wani titi a babban birnin jihar da sunansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

BBC ta rahoto cewa, Shagalin kwana dayan zai bada bayani kan rawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka wurin shugabanci a Afrika ta kudu ballantana Guinea Bissau, shawarwari a kai a kai da kuma nasihohi ga shugabanni kan zaman lafiya, siyasa nagarta da kuma tabbatar da tattalin arziki mai karfi.

Buhari ya dawo Najeriya daga Madrid

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga birnin Madrid.

Kara karanta wannan

Kada Kuji Tsoron Za'ai Fari Ko Karancin Abinci, Mun Tanadi Filayen Noma - NALDA

Shugaban kasan ya dawo daga babbar birnin kasar Andalus, Madrid, kuma ya sauka a Abuja bayan ziyarar kwana 3 da ya kai.

Shugaban ya tashi daga Torrejon Airbase, Madrid, wurin karfe 8 na safiyar Juma'a, kuma ya sauka bayan Sallar Juma'a, hadiminsa, Buhari Sallau ya bayyana.

A kwanaki 3 da yayi a birnin Madrid, Buhari ya gana da Shugaban kasar Andalus, Pedro Sanchez tare da Sarkin kasar King Felipe VI.

A ganawarsa da Shugaba Sanchez; Najeriya da Andalus sun saka hannu kan yarjejeniya tara wanda ya hada da yarjejeniyar mikawa juna mai laifi, matsalar rashin tsaro, harkokin al'adu da Kimiya da fasaha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel